AIWATAR DA SHARI’AR MUSULUNCHI A NIGERIA: NASARORI DA MATSALOLI

Leave a comment

SHIMFIDA

Abu ne sananne a wajen manazarta tarihi cewa, babu wani lokaci da yan Adam suka sami rayuwa nagartacciya wadda take cike da farin ciki da Jin dadi tare kuma da walwala da samun ci gaba a cikin aminci da kwanciyar hankali ga samuwar ‘yanci da adalci hade da kaunatayya a tsakanin mutane kamar lokutan da aka dabbaka Shari’ar Musulunci.
Kasancewar shariar Musulunci ita ce jigo a wajen gyara Rayuwar Dan Adam ya sanya Allah madaukakin sarki ya ba ta cikakken muhimmanci da kulawa a cikin littafinsa Mai albarka. Idan muka duba a cikin Alkurani zamu ga zancen aiwatar da Shari’a a cikin surori sama da guda 50, kuma ayoyin da suka yi wannan maganar sun zarce aya 200.
Aiwatar da Sharia ga musulmi ba zabi ba ne, tilas ne. Domin kuwa Allah mahaliccinmu shi kadai yake da ikon ya zartar da hukunci ga Rayuwar bayinsa, kamar yadda ya ce:
((ان الحكم الا لله امر الا تعبدوا الا اياه، ذلك الدين القيم ولكن اكثر الناس لا يعلمون)) يوسف: ٤٠
A wani wurin kuma Allah mabuwayi ya ce:
((ام لهم شركاء شرعوا لهم من الدين ما لم يأذن به الله)) الشورى: ٢١
Saboda haka, duk musulmin da ya yi kalmar shahadaya zama tilas ya karbi Shari’ar Allah a matsayin doka wadda ba zai tsallaka ba.
Allah madaukaki ya zargi masu bin duk wani tsari da ba nasa ba, kuma ya nassanta cewa yin haka shine jahiliyyah.
((الحكم الجاهلية يبغون ومن احسن من الله حكما لقوم يوقنون)) المائدة: ٥٠
Allah Tabaraka Wa Ta’ala bai nemi kawai mu sanya dokokinsa da suka zo ta hannun Manzo a matsayin abin aiwatarwa ba har sai ya kasance ba mu da ‘dar-‘dar a cikin zukata game da duk hukuncin da aka yanke. Ga abinda Allah ya ce Wa manzonsa:
((فلا وربك لا يؤمنون حتى يحكموك فيما شجر بينهم ثم لا يجدوا في انفسهم حرجا مما قضيت ويسلمون تسليما)) النساء: ٦٥
Hukuncin da Alkurani ya yanke karara ga wadanda suka kauce ma Shari’a suka zabi wani tsari daban shi ne:
((ومن لم يحكم بما انزل الله فأولئك هم الكافرون)) المائدة: ٤٤
Mu yi nazarin wadannan ayoyin har wayau:
((ولقد اتينا بني اسرائيل الكتاب والحكم والنبوة ورزقناهم من الطيبات وفضلناهم على العالمين * وأتيناهم بينات من الامر فما اختلفوا الا من بعد ما جاءهم العلم بغيا بينهم ان ربك يقضي بينهم يوم القيامة فيما كانوا فيه يختلفون * ثم جعلناك على شريعة من الامر فاتبعها ولا تتبع اهواء الذين لا يؤمنون * انهم لن يغنوا عنك من الله شيئا وان الظالمين بعضهم اولياء بعض والله ولي المتقين * هذا بصائر للناس وهدى ورحمة لقوم يوقنون)) الجاثية: ١٦-٢٠

GABATARWA
Yau muna a shekara ta 12 kenan da wannan sabon yunkuri na aiwatar da Shari’a a wasu jihohin da ke arewacin Najeriya. Babu shakka wannan bita da ma ita kanta wannan Mukala sun zo daidai Lokacin da ya dace a yi su domin mu auna nasarori da matsalolin da muka samu mu gano hanyar da zamu ci gaba.
To, amma akwai wasu abubuwa da ya kamata mu soma gabatar da su kafin bayanin nasarori da matsalolin wannan tafiya mai albarka.
1. Ma’anar Shari’a:
Da yawan mutane sun dauka cewa Shari’a tana nufin yanke hukunci na ukuba a kan masu laifi. Wannan kuwa takaitawa ne da takurawa ga ma’anar Shari’a. Domin kuwa Shari’a ta hada duk wani tanadin da musulunci ya yi ma dan Adam ta fuskar yadda zai yi alaka da ubangijinsa da yadda zai yi hulda da mutane masoya da makiya. Don haka ta kunshi Ibada da zamantakewa tsakanin jama’a da sha’anin tattalin arziki da siyasa da kome na rayuwa.
2. Manufofin Shari’a:
Jigon manufofin Shari’a shi ne samar da Jin dadi ga dan Adam a duniya da lahira. Wannan kuwa ba zai yiwu ba sai an kiyaye masa addini da zai lamunce masa nagartacciyar rayuwa, an ba rayuwarsa da hankalinsa da mutuncinsa da dukiyarsa kariya. Binciken ‘kwa’kwaf ya nuna cewa duk wata doka ta Shari’ar Musulunci ba ta fita daga manufofi.
3. Fifikon Shari’ar Musulunci a kan Sauran Tsare tsare
Shari’a ba kamar sauran tsare tsaren da yan Adam suka yi wa kansu ba, ita tsarin Allah ce mahaliccinmu wanda ya san kome fai da boye. Don haka:
– Ba zai yiwu ka samu Kure ko kasawa ko jahilci ko zalunci ba a cikin ta.
– Tana daidai da kowane yanayi, da ko wace al’umma, a kowane lokaci
﴿وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلاَّ كَافَّةً لِلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا وَلَكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لاَ يَعْلَمُونَ﴾ [سورة سبأ، الآية 28].

﴿قُلْ يَا أَيُّهَا النَّاسُ إِنِّي رَسُولُ اللَّهِ إِلَيْكُمْ جَمِيعًا…﴾ [سورة الأعراف، للآية 158].

﴿وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلاَّ رَحْمَةً لِلْعَالَمِينَ﴾ [سورة الأنبياء، الآية 107].

﴿تَبَارَكَ الَّذِي نَزَّلَ الْفُرْقَانَ عَلَى عَبْدِهِ لِيَكُونَ لِلْعَالَمِينَ نَذِيرًا﴾ [سورة الفرقان، الآية 1].

وقال الرسول صلى الله عليه وسلم: (كان النبي يبعث إلى قومه خاصة وبعثت إلى الناس عامة).
– Ba zaka samu nakasu ta fuskar an kula da wani sashe a manta wani ba. Don haka ita ba ta bukatar irin constitutional conference da ake Wa tsare tsaren yan Adam akai akai don a shigar da abinda aka manta ko a gyara abinda aka yi kuskure ko a riski wani sabon kalubale.
4. Wajabcin aiwatar da Shari’a baki daya
Shari’ar musulunci tsari ne kammalalle da idan aka yi aiki da wani bangare nasa shi kadai ba tare wasu bangaroran ba ba za a samu cikakkiyar nasarar da ake so ba. Alal misali, Shari’ar musulunci ba ta yin doka a kan wani laifi har sai ta samar da dukan garkuwar da mutane ke bukata wadda zata hana su aukawa a cikin wannan laifi. Akasarin wadanda suke yin sata ga misali ko dai talauci ne yake kai su ko handama da kwadayi ko kuma an zalunce su ne suka kasa kai ga hakkinsu don haka suka auka cikin na wasu mutane. Shari’ar musulunci duk ta magance wadannan matsaloli ta hanyar Zakka da Sadaka da karfafa yin taimako da umurni da yin adalci da gyara dabi’un mutane har su bar sha’awar abinda ba nasu ba.
Haka ita ma Zina, kafin a yanke hukunci a kan mai yin ta sai da aka haramta ko da kusantar ta; aka hana cudanyar maza da mata ko kebantar namiji da mace wadda ba muharramarsa ba ko yin tsiraici da rangwada a wurin tafiya da kashe murya ga mata da makamantansu. Bayan haka kuma sai aka tanadi hanyoyin sawwake aure da na samun abin yi. Duk da haka kuma sai aka tsananta sharudan tabbatuwar ta ta yadda wanda yake son bayyana alfasha a fili ne kawai ake iya saurin kamawa.
5. Aiwatar da Shari’a ba alhaki ne kawai a kan masu mulki da masu ilimi ba. Wajibi ne a kan kowane musulmi ya duba ta wace fuska yake iya bada tasa gudumawa. Kuma nauyin da ke kan kowane musulmi a wajen aiwatar da Shari’a ya dogara ne ga iya ikon da yake da shi. Amma musulmi mafi rauni shine ake bukatar ya bayyana son sa da goyon bayansa ga Shari’a fai da boye.
Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya zargi wasu a kan kin ba Shari’a goyon baya, sune munafukai. Kuma ya rusa aikinsu a kan haka.
((ان الذين ارتدوا على أدبارهم من بعد ما تبين لهم الهدى الشيطان سول لهم وأملى لهم * ذلك بانهم قالوا للذين كرهوا ما نزل الله سنطيعكم في بعض الامر والله يعلم اسرارهم * فكيف اذا توفتهم الملائكة يضربون وجوههم وادبارهم * ذلك بانهم اتبعوا ما اسخط الله وكرهوا رضوانه فأحبط اعمالهم * ام حسب الذين في قلوبهم مرض الن يخرج الله اضغانهم؟ ولو نشاء لاريناكهم فلعرفتهم بسيماهم ولتعرفنهم في لحن القول والله يعلم اعمالكم)) محمد: ٢٥-٣٠

Ya aka yi maganar Shari’a ta taso?
Muna iya cewa aiwatar da Shari’a a wannan marra ci gaba ne da aikin da magabatanmu jagororin addini da malamai na wannan kasa suka soma tun lokaci mai tsawo. Babu shakka anyi malamai masana masu kokarin tabbatar da kafuwar addini da yada shi tun kafin zuwan mujaddidi Usmanu Danfodiyo a wannan kasa. Alal misali akwai irin su Malam Abdullahi bakatsine mawallafin ADIYYATUL MU’UDI da Malam Muhammadu dan Masani mawallafin ALBUZUGUS SHAMSIYYAH sharhin Ashmawi wanda almajiri ne ga fitaccen malamin nan bakatsine Malam Muhammadu dan Marina. Akwai kuma irin su Malamin Hadisin nan na kasar Hausa; Malam Haruna Zazzau da Malam Umar Dan Muhammad At Torodi da Malam Jibril dan Muhammad wanda Sheikh Usman Danfodiyo yake bugun gaba da shi. A wannan zamanin dai har wayau akwai malamai irin su Malam Kabara daga cikin jikokin Ahmad Baba Tumbuktu da alkalin Kano Malam Muhammad bin Abdilkarim Al Magili dan asalin Tilmisan da ire irensu wadanda kirge su yana da wuya.
Malam Magili shine wanda ya rubuta ma sarkin Kano Muhammadu Rumfa wani muhimmin littafi a kan siyasar musulunci da tsarin gudanar da mulki wanda shine irinsa na farko a wannan kasa. Kuma Abdullahi Danfodiyo na yawan cirato maganganunsa a cikin DIYA’UT TA’AWIL da sauran rubuce rubucensa.
To, sai kuma bayyanar mujaddidi Shehu da almajiransa wadanda suka kawo sauyi mai girma kuma mai albarka a wannan kasa. suka dawo da martabar Shari’a kuma Allah ya taimake su da mulki suka dabbaka ta. Almajiran Shehu sun zo daga wurare daban daban irin su Malam Sulaiman daga Kano da Malam Musa daga Zariya da Malam Yakubu daga Bauchi da Modibbo Buba Yero daga Gombe da Malam Ibrahim Zaki daga Katagum da Malam Sambo Digimsa daga Hadejia da sauran su. Kai har mata a wancan lokaci ba a bar su a baya ba wajen yada addini irin su Khadijah da Maryam da Asma’u da Fatima ‘ya’yan Shehu da Malama Aisha ‘yar Malam Kabara wacce take gabatar da tafsirin Alkur’ani a fadar sarkin Kano da dai sauran su.
Wannan shimfida ta tarihi ta gabata ne don mu san cewa sha’anin addinin musulunci da kafuwar Shari’a a kasar nan ba sabon abu ba ne.
Sai kuma abinda ya biyo bayan kafuwar daular. An samu rahoton bayyanar matsaloli da dama wajen aiwatarwa. Amma kuma dai Shari’ar musulunci ita ce kadai dokar da aka amince da ita. Amma bayan zuwan turawa a kasar nan da kama madafan iko da suka yi sai suka yi iya kokarinsu domin su canja sha’anin Shari’a amma sai suka lura da yadda Shari’a take a cikin jini da tsoka ga jama’a. Don haka sai suka kafa kotuna da zasu aiwatar da hukunce hukuncen Shari’a a iya inda suka amince suke ganin bai ci karo da hankulansu ba wato abinda ake kira Al Ahwalus Shaksiyyah.
Sai kuma tasirin da turawa suka bari kafin su tafi a cikin al’adunmu da tunaninmu. Wannan wani abu ne da magana a kan sa zata tsawaita wajen gano yadda suka nisanta mu daga Shari’ah.
Shari’ar musulunci kenan ba bakuwa ba ce a kasar nan. Kuma cikin hikimar Allah sai aiwatar da Shari’a da koma ma tsarin musulunci a wannan karni ya zo ta inda ba a tsammani. A daidai Lokacin da kasar nan take tafiya a kan tsarin dimukradiyya. Sannan ya zo cikin ruwan sanyi da lumana a matsayin wata bukata ta al’umma. Wannan sai ya bamu darussa masu dinbin yawa. Daga cikin su:
1. Karfin tasirin addini a cikin zukatan mutane la’akari da irin goyon baya da karbuwar da Shari’a ta samu.
2. Yiwuwar aiwatar da Shari’a a karkashin tsarin dimukradiyya kafin samuwar cikakken tsarin musulunci wanda zai tabbata ga baki dayansa cikin yardar Allah a nan gaba. A nan sai mu tuna da yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya yarda da zama memba a cikin kwamitin da aka Kira HILFUL FUDUL a zamanin jahiliyyah tare da kasancewar sa ya kaurace ma dukan al’amurran jahiliyyah, amma shi wannan tunda ya dace da manufofin rayuwarsa sai ya shiga aka yi da shi.
3. Kuma ya nuna mana cewa, abinda bai samu gaba daya ba babu laifi idan an fara yin sashensa kamar yadda Najjashi sarkin Habasha ya musulunta a zamanin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam amma bai iya bayyana musuluncinsa a fili ba balantana zancen aiwatar da shi a kan talakawansa amma kuma duk da haka ya ci gaba da Taimakon musulunci ta wasu fuskoki da yake iyawa.
4. Har wayau aiwatar da Shari’a ya bamu darasi babba shine cewa, duk Lokacin da al’umma take da kuduri da cikakkaiyar azama ta kawo gyara to, abu ne mai yiwu idan an nemi Taimakon Allah.

NASARORIN AIWATAR DA SHARI’A
1. Haduwar kan musulmi da aka samu na wani dan lokaci wanda duk da yake bai dore ba amma ya bar tasiri mai yawa. Darasin da ke cikin wannan shine cewa, a duk Lokacin da akwai kalubale a gaban musulmi akwai yiwuwar su hadu su samar da wata manufa hadaddiya kamar irin halin da muke ciki a yau.
2. An samar wa Shari’a wani gurbi a doka wanda zai hana tsangwama ga duk wata doka ta musulunci da za a aiwatar.
3. Samar da hukumomin aiwatarwa (Hisba, Anti corruption, gyara kayanka, a daidaita sahu, min. 4 religious affairs) wadanda a da ba a tunanin zasu iya kafuwa.
4. Alakanta hukuma da addini. A can baya abu ne da ake tsoro. Amma a yau kowace gwamnati na iya fitowa karara ta yi abu saboda musulunci koda kuma har ta yi alfahari yin hakan.
5. Raguwar Ayyukan barna a wasu jihohi ta yadda har alkaluman kididdiga ta nuna raguwar cututtuka a jihohin da aka aiwatar da Shari’a saboda reguwar Ayyukan assha a cikin su.
6. Karuwar ilimi da fahimtar jama’a a kan Sharia. Domin kuwa an yi nazarce nazarce da wallafe wallafe da dama, an gabatar da karatuttuka da muhadarori da wa’azoji da darussa masu dinbin yawa a kan wannan.

MATSALOLIN DA AKA CI KARO DA SU
Shari’a ta gamu da tarnaki da samun cikas daga bangarori dama wadanda suka hada da makiya na ciki da na waje. Ta yadda aka mayar da ita wani mataki na bayyana a dawa da musulunci da dokokinsa. Alal misali, wace bajinta ce Safiya ta yi wadda ta sa aka mayar da ita a wancan lokaci a cikin kanun Labarin duniya na dukan manyan tashoshin duniya?
An yi ta sukar Shari’ar musulunci da cewa kauyanci ce, ba ta dace da zamani ba, akwai rashin tausayi a ciki da sauransu.
Gaskiyar magana ita ce ko don matsalar tattalin arziki bai kamata muyi tsammanin kasashen yamma su kyale mu mu aiwatar da Shari’a salun alun ba. Domin kuwa duk arzikin duniya yana shimfide ne a kasashen musulmi. Idan muka aiwatar da Shari’a bayan bunkasar arziki da zamu samu to, su fa zamu yanke da tattalin arzikinsu Wanda ya dogara a kan RIBA. Sannan zamu zama masu hankalin da yawo da hankalinmu da suke yi ba zai yiwu ba.
2. Akwai kuma tarnaki na constitution shi kansa da wasu sake-saken layi da karara suke cin karo da Shari’a.
3. Wasu masu son zuciya sun so suyi amfani da wannan su zafafa rikon da ke akwai a tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya. Sai aka nuna masu cewa yin Shari’a na sa a shiga cikin hakkinsu. Abinda ya biyo bayan kuma duka mun sani.
4. Akwai matsalar tsaro ga ita Shari’a din kanta. Jami’an tsaro na kasa duka mallakar gwamnatin tarayya ne. Ba ‘yan sanda ga jihohi. Amma duk da haka, samar da hukumar Hisba na daga cikin abinda yake rage kaifin wannan matsala.
5. Rashin Isasshen tanadi don dorewa da ci gaba da aiwatar da Shari’a. Muna a zamani na wayewa da fadadar sha’anin kimiyya da fasaha. Ya kamata sha’anin aiwatar da Shari’a ya ci moriyar wannan ci gaban da Allah ya kawo. Amma sai ka ga ana amfani da hanyoyin tuka-tuka (sunan wani famfo tsohon yayi) wajen lamurran da suka shafi Shari’a. Wannan ba zai rasa dangantaka da cewa wasu mahukunta Shari’ar ta zame masu dole ba amma ba don tana cikin ajandarsu ba da kuma abinda zamu kawo a nan gaba na rashin cancantar wasu jami’an gudanarwa.
6. Takaita aikin Shari’a ga wasu hukumomi na musamman. Misali zaka taras da cewa, hukumomin aiwatar da Shari’a a kowace jiha irin su ma’aikatar la irfan addini, Hukumar Zakka, Hukumar Hisba da sauransu suna aiwatar da Shari’a, amma idan ka je ma’aikatar lafiya ko ta ilimi ko aikin gona ba zaka ga aiwatuwar Shari’a ba.
7. Rashin shugabantar da wadanda suka cancanta kuma suke da kwarewa a wasu daga cikin hukumomin aiwatar da Shari’a. Wannan ya kawo rashin samun ci gaba a wasu jihohi musamman inda na ba wa al’amarin muhimmanci, an ba da kudi, an ba su iko amma ba a saka wadanda suka dace kuma suke iyawa ba.
8. Wasu na ci da Shari’a. Wannan ya jawo zubewar martabar wasu malamai da aka dora ma alhakin aiwatarwa.

Shawarwari:
1. Dole ne a dauki matakan wadatar da jama’a da kula da inganta rayuwarsu. Yin wannan shi ma Shari’a ne. Kuma shine abinda zai taimaka ainun wajen yakar wasu miyagun dabi’u da hukumomin aiwatar da Shari’a suka dukufa a kai.
2. Lalle ne a sanya zancen aiwatar da Shari’a a dukkan ma’aikatu da wurare na gwamnati da wadanda ma ba na gwamnatin ba. A inganta shiraruwan gyara Tarbiyya irin su A DAIDAITA SAHU da makamantansu.
3. A samar da hukumomi masu karfi da kuma kwararrun manazarta wadanda zasu rinka bincike da wallafa bayanai a kan hanyoyi bunkasa Shari’a.
4. A kara inganta matakan ilmantarwa irin wannan bita, a shirye tafiye tafiye zuwa kasashen da suka yi nisa wajen zartar da dokokin musulunci domin amfani da nasu dabaru da hanyoyi ci gaba.
5. A samar da ingantacciyar hanyar sadarwa tsakanin hukumomin da ke aiwatar da Shari’a na jihohi daban daban.
6. A tabbatar da an shugabantar da wadanda suka dace kuma suke himma ga duk hukumomin da ke da alaka da aiwatar da Shari’a.
7. Hukumar Hisba: A inganta ta sosai, a samar da horarwa isasshiya ga ma’aikatanta, a basu hurumi Mai karfi wajen yakar fitsara da shashanci a tsakanin al’umma.
8. Hukumar Hisba ta sanya hikima wajen gudanar da lamurranta. Ta fuskanci ilmantarwa da nasiha ga jama’a fiye da daukar matakin hukuntawa. Ta kuma bi abubuwa daki daki tana la’akari da yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya bi mutane a hankali har suka mika wuya. Sannan ta bude kofofinta don karbar shawarwari daga jama’a.

Daga karshe..
Wannan lamari fa addini ne. Kuma duk wanda Allah ya ba shi wata dama ta taimakawa domin ci gaban Shari’a da daukakar ta, to Allah ya bude masa wata babbar kofa zuwa aljanna. Don haka kada ya yi sakaci da ita.
Allah ya yi mana jagora, ya tsarkake zukatanmu, ya kyautata ayyukanmu, ya sa mu yi karshe mai kyau.
Na gode da wannan dama da aka ba ni.
وسبحانك اللهم وبحمدك اشهد الا اله الا انت أستغفرك وأتوب إليك.

SANIN MUHIMMANCIN LOKACI

1 Comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ba wani mutum a duniya da ya kamata ya san muhimmancin lokaci kamar musulmi. Idan musulmi ya wayi gari abu na farko da zai yi shi ne sallar asuba, can bayan rana ta gota ya yi azahar.. haka har wuninsa ya kare yana bibiyar lokuta don ya gana da ubangijinsa. A sati kuma akwai sallar jumu’ah.. a shekara akwai watan azumi, akwai idi, akwai layya, akwai aikin hajji. Idan musulmi yana da jari kuma akwai fitar da zakkah duk shekara. Allah ya rantse mana da lokaci don mu san muhimmancinsa. Lokaci ga dan adam shi ne jarinsa, kai ma dai shi ne rayuwarsa. A cikinsa ne kake murna ko ka samu damuwa. A cikinsa ne kake ciwo ko ka samu lafiya. A cikinsa ne kake talauci ko ka samu arzikin duniya. A cikinsa ne kake shuka alheri ka girbe shi lahira ko ka shuka sharri ka same shi can yana jiran ka gome alkiyama. Don haka a cikin lokacin duniya ne ake samun aljanna ko a fada cikin jahannama. Allah ya kiyaye mu. Lokaci ya fi komi saurin wucewa. Ba ya jira, kuma in ya tafi ba ya dawowa. Sannan kuma Allah bai sanar da kowa lokacin da ya diba ma sa ba. Lokacin da Allah ya ba ka shine tsawon shekarun rayuwarka. Idan ka kwantar da hankalinka sai ka ga dan lokaci ne da ba ya da yawa. Wanda aka ba shi shekaru sittin misali nawa ne za a cire daga ciki na kuruciyarsa? Nawa ne yake kararwa a barci? Nawa ne adadin kwanuka marasa amfani a cikin su? Dan Adam ya kan yi nadama a kan lokacinsa da ya wuce a wurare muhimmai guda biyu: Na farko: Idan mala’ikan mutuwa ya damke shi, ya hakikance cewa tilas zai bar duniya a nan ne yake cewa: Ya ubangiji ku dawo da ni. Domin kila in yi aikin kwarai a cikin abinda na bari. Ina! Wata magana dai ce da shi yake fadar ta, kuma a bayan su akwai rayuwar barzahu da zasu yi har zuwa ranar da za a tashe su. Suratul Muminun: 99-100 Wuri na biyu: Shi ne idan aka yi tashin alkiyama, kowa ya ga sakamakonsa, aka yanke ma kowa hukuncin in da zai zauna. A nan ne dan adam ke cewa: Kuma da zaka ga kangararru sun sunkuyar da kawunansu a wurin ubangijinsu, (suna cewa): “Ya ubangijinmu! Mun fa gani kuma mun jiya, to, ka mayar da mu mu yi aikin kwarai, mu fa tabbas mun gano gaskiya”. Kuma da mun so da mun bai wa kowane mai rai ikon shiriya, amma maganarmu ta riga ta tabbata cewa, lalle sai mun cika wutar jahannama da aljanu da mutane baki daya. To, ku dandani azaba don mantawar da kuka yi da haduwarku ta wannan rana, mu ma mun manta da ku, kuma ku dandani azaba ta din-din-din saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa. Suratus Sajdah: 12-14 Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya fada mana cewa, akwai ni’imomi guda biyu da ake kwaruwar dan adam a kan su; lafiya da kuma lokaci. Dalilai uku ne ke sa a kwari mutum game da sha’anin lokaci. Ko dai ya kasance bai yi cikakken amfani da lokacin ba ta hanyar yin abinda ya kamata wanda zai samu babbar lada, ko kuma ya kasa yin aikin lada sam sam, ko kuma a cikin lokacin ya yi aikin zunubi. Mutane sun kasu kashi kashi dangane da lokaci. Wani za ka ga mafi yawan lokacinsa yana cike da abubuwa ne masu amfani, wani kuma duk lokacinsa na sharholiya ne, wani shi kuma bai ma san ya zai yi da lokaci ba! Matsalar wani ita ce bai tsara ma rayuwarsa kome ba, wani kuma bai san muhimmancin lokacin ba. Wani ya sani amma bai da karfin zuciya da kwarin guiwa na maida hankali ga abinda ke amfaninsa. Yana da kyau mu duba rayuwar magabata mu ga yadda suke cin moriyarsa. Abdurrahman bin Mahdi ya bada labarin malaminsa Hammad bin Salamah ya ce, da an ce ma Hammad ga alkiyama nan za ta tsayu bai da yadda zai kara bisa ga aikin da ya ke yi. Ba zamu yi mamakin wannan maganar ba in muka san cewa malam Hammad ya rasu yana cikin sallah. Saurari wani dalibin ilimi abinda Abu Hatim Ar-Razi Rahimahullah abinda yake cewa: “Mun nemi malam Ka’anabi ya karantar da mu Muwadda sai ya ce to ku zo da safe. Sai muka ce masa da mun yi asuba wurin malam Hajjaj muke zuwa. Ya ce, to ku zo in kun kare. Muka ce sannan muke zuwa wurin malam Muslim bin Ibrahim. Ya ce to ku zo in kun gama. Muka ce ko da muke gamawa azahar ta yi, sannan muke karatu ga Abu Huzaifa. Ya ce, to, ku zo bayan la’asar. Muka ce, makarantar Arim. Ya ce to ku zo bayan magariba. To, daga nan muka rinka zuwa wurin sa idan an yi magariba sai ya fito ana sanyi ya nadiye kansa ya yi ta karantar da mu har illa mashaAllahu”. Ta hanyar amfani da lokaci ne kawai ake iya fito da baiwa iri iri da Allah ya yi wa dan adam. Bincike ya nuna cewa akasarin mutane ba su amfani da kashi 25 cikin 100 na baiwar da Allah ya ba su. Yaron da ya fadi jarabawa kuma ya rufe aji yana iya zama na daya ba a makarantarsu kawai ba a fadin jiha gaba daya inda an yi kokarin fitowa da baiwar da Allah ya ba shi. Shiriritaccen da zaka gan shi yana kashe wando a bakin titi yana iya zama babban malami ko babban mawallafi ko kwararren likita ko gogaggen dan siyasa ko fitaccen dan kasuwa. Amma an watsar da baiwar da Allah ya ba shi, shi ya sa ya lalace. Wanda ya zo na baya a wajen tsera ko gasar karatun alkur’ani yana iya zarce kowa in da an tona baiwar Allah da ke tattare a cikin sa. Kana iya gwada wannan ga dan takara a wajen tserar gudu idan ya kasa, ya koma baya har ya kai ga faduwa saboda gajiya. Idan likitoci suka auna shi a lokacin zasu ce mana akwai sauran karfi da kuzari mai yawa a jikinsa amma yana bukatar abinda zai zakulo wannan karfin. Ya zamu gane wannan? Mu sakar masa zaki ko maciji misali. A nan ne zaka sha mamaki. Suna yin arba da zaki zaka ga ya tashi ya ruga da gudu, irin gudun da can da farko ma bai yi shi ba. Me ya tono wannan kuzari na gudu daga jikinsa? Daga sama aka sauko masa da shi? A’a. Daman yana nan cikin jikinsa amma yana neman abinda zai motsa shi! Wannan shi zai fassara maka irin albarkar rayuwar magabata wajen jihadi da karantarwa da rubuce rubuce da makamantansu. Sun sanya wata manufa a gaban su ita ce neman yardar Allah. Wannan manufa sai take fitar da iyakar abinda yake yiwuwa na baiwar Allah da ke cikin su. In ba don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ba da su sayyidina Umar da Ibnu Mas’ud da Khalid bin Walid da sauransu duk iyakar su su zamo makiyaya ko ‘yan kasuwa ko ‘yan tauri ko wani abu mai kama da wannan. Amma da aka samu jagora cikakke mai manufa sai ya fito da ikon Allah a cikin su. Nan take kowanensu ya taka rawa mai muhimmanci a tarihin duniya. Wani daga cikin magabata ke cewa, wani lokaci sai bacci ya fara dauka ta, ina cikin jin dadinsa sai in tuna da wuta da aljanna. Idan na tuna haka sai in ga na zabura kamar zaki na tafi zuwa kiyamullaili. Ko kun ga yadda tsayayyar manufa take sa a kula da muhimmancin lokaci? Fetur idan aka zubar da shi ga kasa sai kasa ta shanye shi bai amfani kowa ba. Amma in da an zuba shi a mota fa? Wannan shi ne misalin hikimomin Allah da bamu yi amfani da lokaci muka ci moriyar su ba. Wannan kuma shi ne sirrin da ya sa idan an yi yaki musulmi ke galaba a kan kafirai. Allah Ta’ala ya ce: Kuma kada ku yi rauni wajen yakar mutanen, in har kuna jin radadi, to hakika su ma suna jin radadi kamar yadda kuke ji, kuma kuna fatar samun abinda ba su fatar samun sa daga wurin Allah. Kuma Allah ya kasance mai cikakken sani, mai cikakkiyar hikima. Suratun Nisa’i: 104 A wata ayar kuma Allah ya ce: Kuma kada ku yi rauni, kada ku yi bakin ciki, domin ku ne madaukaka in har kun kasance muminai. Suratu Ali Imran: 139 Wani malami ya tsaya a gaban ‘yan wasa suna ta sharholiyarsu. Sai aka gan shi yana jin haushi yana ciza yatsa. Don me? Ya ce, wallahi na so a ce lokaci kaya ne, sai in sayi na wadannan don ba ya da amfani gare su. Ya ku bayin Allah! Ga wasu muhimman shawarwari da zasu taimaka mana wajen kula da lokaci: 1. Kada ka yarda ka bar wani lokaci ‘yamti, domin wannan ba dabi’ar mumini ba ce. Allah Ta’ala ya ce: “Idan ka gama al’amurran duniya, to ka kafu wajen ibada. Kuma ka yi kwadayi zuwa ga ubangijinka” Suratus Sharh: 7 -8 Da zaran ka samu lokacin da ba komai da zaka yi, samar masa wani abinda zai amfane ka. Misali lokacin jiran wani, kamar jiran likita a asibiti, ko layin shiga mota, ko kuma kan hanya daga wani gari zuwa wani gari ko wata unguwa zuwa wata unguwa. A lokacin da kake tuka babur ko aka dauka a kansa zuwa kasuwa. A lokacin da kake shago amma ba wani abokin ciniki tare da kai. A duk irin wadannan lokuta kana iya kago wani abu da zai amfane ka kamar yin zikiri ko karanta wani littafi ko kuma wata tattaunawa mai muhimmanci da wani wanda kake tare da shi. Da wannan ma’aikaci na iya cin moriyar abinda ya yi rara na lokacinsa. Dan kasuwa ma haka. Mai achaba da mai lodi da kafinta da mai kasa kaya a titi duk suna iya amfani da lokutan rara a wajen ambaton Allah da makamantansa. Ibnu Taimiyyah Abdussalam yakan ce ma dansa Ibnu Taimiyyah Ahmad: “Zo ka yi karatu kusan da ban-daki kafin na fito” don ya saurari karatu a yayin da yake biyan bukata, gudun kada lokacinsa ya tafi a banza a daidai wannan lokaci. 2. Yi kokari a kullum ka gabatar da abinda ya fi muhimmanci. Idan ayyuka biyu suka hadu babba da karami ka fara gabatar da babba. Idan kuma dayansu yana amfaninka ne kai kadai dayan kuma yana amfanin jama’a, fara yin mai amfanin jama’a tukuna. Kamar sallar nafila da karantar da mutane. Idan kuma aiki daya yana da lokaci mai wucewa dayan kuma ana iya yin sa a koyaushe to, fara gabatar da wanda lokacinsa ke wucewa. Kamar addua a lokacin ijaba. 3. Ka auna duk maganar da zaka yi don ka tantance amfaninta ko cutarwarta. Idan ka yarda ba ta da amfani sai ka bar ta ka yi wata ko kayi shiru don ka tsira da lokacinka. 4. Yi kokari ka gano lokutan da kake tozartawa a wuni. Misali, daga sallar asuba zuwa karfe goma, awa ne? Wane amfani suke maka? Kar ka manta cewa, kafin wannan lokaci ka share dare watakila kana barci. Tsakanin magariba da isha’i me kake yi? Daga isha’i zuwa shiga bacci fa? Idan ka gano wadannan lokutan sai ka tsara yadda za ka rage tozarta su. 5. kada ka bari mutane su rika sitarin lokacinka. Duba misali yadda Imamul Bukhari yake yi idan ya yi bako mai nauyi. Abinda yake yi shi ne sai ya dauko littafinsa ya ce ma bakon yana da kyau mu karanta wannan domin mu amfana. Shi kuma Ibnu Akil Al-Hambali idan ya yi irin wadannan baki sai ya dauko alkalumansa na rubutu ya ce su taya shi fekewa. 6. Tuna mutuwa na taimaka maka ainun wajen kula da lokacinka. Duk matafiyi idan ya ci rabin hanya zai ji cewa ya kusa kai. Amma a mas’alar rayuwa da mutuwa ba mu tuna haka. Sai ka ga mutum in ya yi shekaru talatin yana ganin tukuna bai yi kome ba. Shi ya sa ake cewa mafi yawan mutane suna mutuwa ne a cikin kuruciya, don ba a dauka sun kai lokacin mutuwa ba. Rayuwar dan adam ba ta da tsawo. Akwai halittu na daji da ke kai shekaru 200 zuwa 300 ko abinda ya fi haka. A bishiyoyi ma akwai wadanda su ke kunne ya girmi kaka. Su duwatsu ba a ma maganar su. Don haka babu mamaki ka ga shekarunka sun kare nan take. Samu wata rana ko da a cikin wata ne ka je ziyara makabarta kai kadai ka tsaya ka kalli wadanda ke kwance. Ka tambaye su, mene ne gurinku? Me kuke fata a yau? Ba zasu ba ka amsa ba. Amma ka sani da zasu buda baki da zasu ce, muna son mu dawo duniya mu ci ribar lokaci. 7. Sanin cewa bayan mutuwa akwai tambaya. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: “Ba wanda zai daga kafarsa a ranar alkiyama har sai ya amsa tambayoyi guda hudu: Ta farko: Rayuwarsa a ina ya karar da ita? Ta biyu: Kuruciyarsa a kan me ya tafi da ita? Ta uku: Abinda ya sani ko ya yi aiki da shi? Ta hudu: Dukiyar da ya samu a duniya, ta ina ya same ta kuma ta yaya ya kashe ta? Ya ku ‘yan uwa musulmi! Muna gaf da shiga wani wata mai albarka wanda masu dabara suke cin kasuwar lahira a cikinsa. Watan Ramadhan wanda ayyukan lada suka fi komi kadari a cikinsa. Watan da ke da Lailatul kadari a cikinsa. Wane irin shiri muka yi domin tarbonsa? Wace ajenda muka sanya ma kanmu don ganin mun amfana da shi watakila shi ne na karshen da wasunmu zasu gani? Wasu an yi na bara da su amma ba za ayi na bana da su ba. Wasu ma daga cikinsu yanzu an rabe dukiyoyinsu, an aure matayensu, an rufe shafin tuna su. Suna can a tsakanin ayyukansu da suka shuka a nan duniya. Mu ja damara ya ku ‘yan uwa, mu sa himma, mu shirya ma wannan wata duk abinda muke iyawa. Mu yi tattali na yin azumi da tarawihi da halartar tafsiri da yin sadaka da sada zumunta da yin umra ga masu hali da I’itikafi da duk abinda muke fatar ya sada mu da Allah. Ya Allah ka yi muna dace, ka sa mu cikin bayinka salihai, ka isar da mu wannan wata, ka sa ya zama watan diyautawa da gafara a gare mu.

DAGA MASALLACIN SAYYIDINA ABU HURAIRA ( RA), SOKOTO Yan uwa da muke tare a wannan dandali yau ma ba ni a garin Sokoto, kuma Na’ibi na daya Sheikh Muhammad Sani Abdullahi zai jagoranci sallar jumu’ah. Na debo maku daga cikin taskar hudubobin da suka gabata wacce aka gabatar a ranar 21 ga Sha’aban 1432H (22/7/2011) mai taken:

HADARIN ZALUNCI

Leave a comment

DAGA MIMBARIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Addinin musulunci addinin Allah ne da ya shinfida hanyoyin zaman lafiya da jin dadin rayuwa. Daga cikin manya manyan dokokin ubangiji shi ne ya wajabta adalci kuma ya haramta cuta. Wadannan dokokin Allah ya dora su har ga kansa. Don haka, Allah Tabaraka Wa Ta’ala ba ya zalunci kuma ba ya bari a zalunci bayinsa. Allah Ta’ala yana cewa:

{إِنَّ اللَّهَ لاَ يَظْلِمُ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ} [النساء:40].
{وَمَا اللَّهُ يُرِيدُ ظُلْماً لّلْعَالَمِينَ} [آل عمران:108].
A hadisul kudsi ga abinda Allah ke cewa:
((يا عبادي، إني حرمت الظلم على نفسي، وجعلته بينكم محرماً، فلا تظالموا)) الحديث.
A cikin dukkan addinan da Allah ya saukar ba in da bai haramta zalunci ba, Gashi ko dan adam an halicce shi da son yin zalunci da cuta kamar yadda Allah ya ce:

{إِنَّ الإنْسَانَ لَظَلُومٌ كَفَّارٌ} [إبراهيم:34].
{إِنَّا عَرَضْنَا الأمَانَةَ عَلَى السَّمَاواتِ وَالأرْضِ وَالْجِبَالِ فَأبَيْنَ أَن يَحْمِلْنَهَا وَأَشْفَقْنَ مِنْهَا وَحَمَلَهَا الإِنْسَانُ إِنَّهُ كَانَ ظَلُوماً جَهُولاً} [الأحزاب:72].
Al-Hafiz Ibnu Kayyim al-Jauziyyah yana cewa: Duk asalin kowane alheri abu biyu ne: Ilmi da adalci. Haka kuma duk asalin kowane sharri daga jahilci ne da zalunci. Idan Allah yana son alheri ga mutum sai ya sanar da shi abinda ke amfaninsa, sai ya kawar da jahilci, sannan ya ba shi ikon amfani da shi sai ya gusar da zalunci. Duba Igathatul Lahfan (2/136-137).
Hadarin zalunci ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya shelanta haramcinsa a taro mafi girma kuma mafi daraja da musulmi suka taba yi a zamaninsa. Hadarin zalunci yana kara hauhawa idan ya kasance ya auka ma jama’a masu yawa, ko wadanda aka sani ko wadanda ba a sani ba. Wannan shi ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya tsananta maganar cin dukiyar ganima kafin a raba ta kuma ya ce, { عار ونار وشنار على أهله يوم القيامة } kuma da aka kashe wani yaronsa da ake ce ma Mid’am sahabbai suka ce, muna yi masa murnar shiga aljanna, sai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, sam. Na rantse da Allah yana can yana ci da wuta a kan bargon da ya dauka daga cikin ganimar Khaibar. Da jin haka sai wani sahabi ya yi sauri ya dawo da saitin takalma guda daya da ya dauka. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, ka kuru, domin da sun zame ma ka takalma biyu na wuta.
Kafin mu fadi irin hadurran da ke tattare da zalunci bari mu diba irin tsawatawar da Allah Ta’ala ya yi dangane da shi:
{ وَالظَّالِمِينَ أَعَدَّ لَهُمْ عَذَابًا أَلِيمًا}. وقال تعالى: {وَمَن يَظْلِم مِّنكُمْ نُذِقْهُ عَذَابًا كَبِيرًا}.
{وَتَرَاهُمْ يُعْرَضُونَ عَلَيْهَا خَاشِعِينَ مِنَ الذُّلِّ يَنظُرُونَ مِن طَرْفٍ خَفِيٍّ وَقَالَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ الْخَاسِرِينَ الَّذِينَ خَسِرُوا أَنفُسَهُمْ وَأَهْلِيهِمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ أَلَا إِنَّ الظَّالِمِينَ فِي عَذَابٍ مُّقِيمٍ}.
{إِنَّا أَعْتَدْنَا لِلظَّالِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمْ سُرَادِقُهَا وَإِن يَسْتَغِيثُوا يُغَاثُوا بِمَاء كَالْمُهْلِ يَشْوِي الْوُجُوهَ بِئْسَ الشَّرَابُ وَسَاءتْ مُرْتَفَقًا}.
Kuma shi zalunci ba ya da kadan. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya ci zalun wani mutum da karfi Allah zai haramta ma sa aljanna ya wajbta ma sa wuta. Sai wani ya ce, ya manzon Allah, ko da abin kadan ne? sai Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce, “Ko da karen aswaki ne”. Muslim ya ruwaito shi.

Daga cikin manyan bala’oin da zalunci ke haifarwa akwai:

1. Hana zaman lafiya da ci gaba
الَّذِينَ آمَنُوا وَلَمْ يَلْبِسُوا إِيمَانَهُمْ بِظُلْمٍ أُولَئِكَ لَهُمُ الْأَمْنُ وَهُمْ مُهْتَدُونَ

2. Gamuwa da hukuncin Allah. Hadisi ya bayyana cewa, Allah Ta’ala azabta wata macce a kan kyanwa. To, in aga bawan allah mummuni, ina kuma ga al’umma mai dinbin yawa wadanda kila ba ka san iyakar su ba!!
3. Allah ba ya son azzalumai:
وَتِلْكَ الْأَيَّامُ نُدَاوِلُهَا بَيْنَ النَّاسِ وَلِيَعْلَمَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَيَتَّخِذَ مِنْكُمْ شُهَدَاءَ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الظَّالِمِينَ

4. Kuma ya debe ma azzalumai albarka أَلَا لَعْنَةُ اللَّهِ عَلَى الظَّالِمِينَ
5. Zalunci yana haifar da duhu ga mai yin sa ranar alkiyama, ranar da kowa ke bukatar haske don tsallake siradi. Kamar yadda hadisi ya zo cewa:
((الظُّلم ظلماتٌ يوم القيامة)) (أخرجه البخاري (5/100 الفتح) ومسلم (2579) عن ابن عمر).

6. Zalunci yana janyo halaka ga al’umma
{وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُواْ وَجَاءتْهُمْ رُسُلُهُم بِالْبَيّنَاتِ} [يونس:13].
(( فَلَمَّا نَسُواْ مَا ذُكِّرُواْ بِهِ فَتَحْنَا عَلَيْهِمْ أَبْوَابَ كُلِّ شَيْءٍ حَتَّى إِذَا فَرِحُواْ بِمَا أُوتُواْ أَخَذْنَاهُم بَغْتَةً فَإِذَا هُم مُّبْلِسُونَ * فَقُطِعَ دَابِرُ الْقَوْمِ الَّذِينَ ظَلَمُواْ وَالْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ )) (44-45:الانعام).
((وَلَقَدْ أَهْلَكْنَا الْقُرُونَ مِن قَبْلِكُمْ لَمَّا ظَلَمُواْ)) (13:يونس).
(( وَتِلْكَ الْقُرَى أَهْلَكْنَاهُمْ لَمَّا ظَلَمُوا وَجَعَلْنَا لِمَهْلِكِهِم مَّوْعِداً )) (51: الكهف).
7. A kullum wanda ke zalunci ba ya rabuwa da Allah ya isa. Wannan ko yana da matukar hadari. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma Mu’az bin Jabal Radiyallahu Anhu: «Ka kiyayi «Allah ya isar» wanda aka zalunta, don ba ta da shamaki tsakanin ta da Allah». Haka kuma sayyidina Abu Huraira Radiyallahu Anhu ya ruwaito daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa: «Addu’ar mutum ukku Allah na karbar su: «Wanda aka zalunta da Matafiyi da Mahaifi».
Kana can kana sharar bacci, kana ta sakin hansari, hankalinka a kwance, ba ka tunanin kome, shi kuma wannan bawan Allah yana can yana dako, sai dare ya kai tsakiya ko ya kusa karewa, a cikin duhu zai tashi, cikin natsuwa ya yi alwala ya kabbarta sallah.. idan ya kai goshinsa ga kasa sai ya tartsa ma Allah kuka, a daidai lokacin da Allah ke shelar: «Ina mai kirana in karba ma sa?» «Ina mai neman agajina in agaza ma sa?». Ana haka ne zai kai karar ka ga buwayayyen sarki. Don haka ne sai ka ga kwatsam! al’amarin mutum ya dagule, basirarsa ta toshe, dabararsa ta kare, jarinsa ya kare, ikonsa ya gushe, lafiya ta karanta, jin dadi ya kau, jama’a sun watse, an bar shi da tarin zunubi, da yawan bakin ciki da karancin jin dadi ..Wannan duk karamin aikin Allah ya isa kenan. Wannan shi ne abin da sarki Khalid al-Barmaki ya fada ma dansa lokacin da aka tsare su a kurkuku, yaron ya ce, Baba! dubi halin da muka fito kuma dubi yanayin da muka samu kanmu. Sai sarki Khalid ya ce ma sa, Allah dai ya kiyaye. Watakila wani ne ya yi mana “Allah ya isa» muna can muna bacci. Wani fursuna ya yi ma sarki Khalid bin Abdillah al-Kasari wa’azi mai kama da haka a lokacin yana gwamnan Khurasan sai ya kai ziyara gidan kaso yana raba ma fursunoni kyauta. Da ya kawo ga wannan bawan Allah sai ya ce ma sa: In don ka tausaya kake bayarwa to, tausaya ma kanka daga wanda ka zalunta. Yi hattara da wanda bai da kowa sai Allah, bai da wani makami sai addu’a. Ka sani kofofin sama gaba daya budewa su ke in an ce, “Allah ya isa».

Ga nasihar da wani mawaki ya yi:

لا تظلمنَّ إذا ما كنت مقتدراً فالظلم ترجع عقباهُ إلى الندم
تنامُ عيناك والمظلوم منتبه يدعو عليك وعينُ الله لم تنم
Wani kuma sai ya ce:
أما والله إن الظلم شؤم وما زال المسيء هو الظلوم
ستعلم يا ظلوم إذا التقينا غداً عند المليك من الملوم
8. Azzalumi ba ya taba samun rabauta. Saurari abinda annabin Allah Yusuf Alaihis Salam ya ce a lokacin da matar maigidansa ta neme shi da ya ci amanarsa:
((وَرَاوَدَتْهُ الَّتِي هُوَ فِي بَيْتِهَا عَنْ نَفْسِهِ وَغَلَّقَتِ الْأَبْوَابَ وَقَالَتْ هَيْتَ لَكَ قَالَ مَعَاذَ اللَّهِ إِنَّهُ رَبِّي أَحْسَنَ مَثْوَايَ إِنَّهُ لَا يُفْلِحُ الظَّالِمُونَ))

9. Allah ba ya shiryar da azzalumi
((أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَجَاهَدَ فِي سَبِيلِ اللَّهِ لَا يَسْتَوُونَ عِنْدَ اللَّهِ وَاللَّهُ لَا يَهْدِي الْقَوْمَ الظَّالِمِينَ))

10. Azzalumi zai gamu da gamonsa tun a nan duniya
((فَذَرْهُمْ حَتَّى يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَ يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنْصَرُونَ * وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَلِكَ وَلَكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ))

11. A ranar alkiyama azzalumi yana da ban tausai:
((وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ)) (227: الشعراء) .
{وَلاَ تَحْسَبَنَّ اللَّهَ غَافِلاً عَمَّا يَعْمَلُ الظَّالِمُونَ إِنَّمَا يُؤَخّرُهُمْ لِيَوْمٍ تَشْخَصُ فِيهِ الأبْصَارُ * مُهْطِعِينَ مُقْنِعِى رُءوسِهِمْ لاَ يَرْتَدُّ إِلَيْهِمْ طَرْفُهُمْ وَأَفْئِدَتُهُمْ هَوَاء} [إبراهيم:42، 43].
{مَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ حَمِيمٍ وَلاَ شَفِيعٍ يُطَاعُ} [غافر:18]
{وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ} [البقرة:270]
A rannan ne azzalumi zai nemi ba da fansa da duk abinda ya mallaka, ciki har da dan jarinsa na duniya, kai da ma duk abinda ake so in zai samu. Amma ina!
(( وَلَوْ أَنَّ لِكُلِّ نَفْسٍ ظَلَمَتْ مَا فِي الأَرْضِ لاَفْتَدَتْ)) (54:يونس)
(( وَلَوْ أَنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا مَا فِي الْأَرْضِ جَمِيعاً وَمِثْلَهُ مَعَهُ لَافْتَدَوْا بِهِ مِن سُوءِ الْعَذَابِ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَبَدَا لَهُم مِّنَ اللَّهِ مَا لَمْ يَكُونُوا يَحْتَسِبُونَ)) (47:الزمر) .
12. Ba yadda za a yi a shiga aljanna tare da digon zalunci domin kuwa ko bayan tsallaka siradi ba a shiga aljanna har sai an kawar da zalunci kowane iri, an kwatar ma kowane mai alhaki hakkinsa. Abu Sa’id al-Khudri Radiyallahu Anhu ya karbo daga manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama cewa, “Idan mummunai suka tsallaka siradi za a tsayar da su a kan wata gada da ke tsakanin aljanna da wuta sai a caje su da wasu laifukka na zalunci da suka gudana a tsakanin su. Sai an gama tsarkake su tsabal sannan ayi ma su iznin shiga aljanna”. Sannan manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya yi rantsuwa cewa, idan suka shiga aljanna kowa zai gane gidansa fiye da yadda ya ke gane gidansa na duniya. Sahihul Bukhari (2440). Allah Ta’ala ya yi gaskiya:
وَالَّذِينَ قُتِلُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ فَلَنْ يُضِلَّ أَعْمَالَهُمْ * سَيَهْدِيهِمْ وَيُصْلِحُ بَالَهُمْ * وَيُدْخِلُهُمُ الْجَنَّةَ عَرَّفَهَا لَهُمْ

Ya ku bayin Allah! Da yawa mukan yi kuskure in mun ji ana ruwan ayoyi game da zalunci da azzalumai sai mu ce, sarakuna sun halaka! Kaicon masu mulki! Bone ya tabbata ga alkalai!!! Babu in da ba a iya samun zalunci a cikin zamantakewa ta rayuwa. Akwai zalunci a ciniki, akwai shi a bashi, akwai a kwadago, akwai a auratayya, akwai a makwautaka, akwai malanta. Haka kuma akwai shi a magana, akwai a kallo, akwai har a batun zucci ta hanyar miyagun zace-zace. Idan ka sa mutum aiki ka rage ma sa hakkensa kai azzalumi ne. idan ka yi algussu a cikin sana’arka kai azzalumi ne. Idan ka sare icce wanda mutane suke shan inwa kai azzalumi ne. Idan aka yi yarjejeniya da kai ka saba kai azzalumi ne. Idan ka kwance sharadi kai azzalumi ne. Idan macce ta debi kayan gidan mijinta ba da izninsa ba ita azzaluma ce. Idan miji ya kasa ba matarsa hakken kwanciya ko na abinci ko karantarwa ko kulawa da lafiyarta shi azzalumi ne. Kai, idan ma ya kasa ba ta alhakinta na zaunawa su yi fira, da jiyar da ita dadin rayuwar macce da namiji shi azzalumi ne. Haka kuma azzalumi ne idan ya kasa daidaita alhakin matansa ko ‘ya’yansa. Babu shakka shugaba in ya zamo azzalumi to, hadarinsa ya fi girma wannan shi ya sa za a zo da kowane shugaba koda na mutum goma ne a daure ranar alkiyama sai dai in ya yi adalci adalcin nasa ya warware shi kamar yadda ya tabbata a cikin hadisi. Duba Sahihul Jami’ 5571 da Silsila Sahiha 344.

Zalunci mataki ukku ne:

1. Mafi hadarinsu shi ne wanda ya danganci hakkin Allah kamar Shirka. Sai kuma sauran zunubbai da Allah ya hana.
2. Zaluntar bayin Allah. Mafi hadari daga cikin zaluntar bayin Allah shi ne zubar da jininsu, sannan cin mutuncinsu, sannan kwace ko satar dukiyarsu.
3. Mutum ya zalunci kansa ta hanyar aikata abinda zai halaka shi ko ya sa shi cikin kunci a nan duniya ko a gobe kiyama.
Idan an zalunce ka ya zaka yi? akwai matakai guda uku, wanda duk kayi babu laifi a kanka:

1. Ka rama daidai yadda aka zalunce ka in kana da iko
{وَلَمَنِ انتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُوْلَئِكَ مَا عَلَيْهِمْ مّن سَبِيلٍ} [الشورى:41].

2. Ka roki Allah ya rama maka, ko ya kwatar ma ka hakkinka
{لاَّ يُحِبُّ اللَّهُ الْجَهْرَ بِالسُّوء مِنَ الْقَوْلِ إِلاَّ مَن ظُلِمَ وَكَانَ اللَّهُ سَمِيعاً عَلِيماً} [النساء:148].

3. Ka yafe saboda Allah
خُذِ الْعَفْوَ وَأْمُرْ بِالْعُرْفِ وَأَعْرِضْ عَنِ الْجَاهِلِينَ * وَإِمَّا يَنْزَغَنَّكَ مِنَ الشَّيْطَانِ نَزْغٌ فَاسْتَعِذْ بِاللَّهِ إِنَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٌ

Wadannan matakan gaba daya Allah Ta’ala ya fade inda yake cewa:

{وَالَّذِينَ إِذَا أَصَابَهُمُ الْبَغْىُ هُمْ يَنتَصِرُونَ * وَجَزَاء سَيّئَةٍ سَيّئَةٌ مّثْلُهَا فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ إِنَّهُ لاَ يُحِبُّ الظَّالِمِينَ * وَلَمَنِ انْتَصَرَ بَعْدَ ظُلْمِهِ فَأُولَئِكَ مَا عَلَيْهِمْ مِنْ سَبِيلٍ} [الشورى:39-41].

Ya ku bayin Allah! wanda ya fada a cikin zalunci alhakinsa a kan mu shi ne mu taimake shi. Ya zamu taimake shi? wannan shi ne abinda sahabbai suka tambayi manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama a lokacin da ya ce, “Ka taimaki dan uwanka ko shi ke zalunci ko shi aka zalunta”. Amsar da manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ba su ita ce, taimakon azzalumi shi ne a kange shi a hana ma sa yin zalunci. Allah Ta’ala na iya yi wa azzalumi talala amma ba zai taba kyale shi ba. Sau da yawa kuma Allah ya ke sallade wani azzalumi don ya darkake wani. Kamar yadda madaukakin sarki ya ce:

(( وَكَذَلِكَ نُوَلِّي بَعْضَ الظَّالِمِينَ بَعْضاً بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ)) (129:الانعام)

Don haka ne wani malami ya ce:

وما من يد إلا يدُ اللهِ فوقَها ولا ظالمٍ إلا سُيبلى بظالم

A nan duniya azzalumi na iya samun girma da kima ko don kwadayin abin hannunsa ko don gudun sharrinsa, amma a ranar alkiyama babu wulakantacce marar daraja da kima irin sa. Sai dai yana da kyau mu sani cewa, kome girman zalunci yana da tuba kamar yadda madaukakin sarki ya ce:

{وَمَن يَعْمَلْ سُوءاً أَوْ يَظْلِمْ نَفْسَهُ ثُمَّ يَسْتَغْفِرِ اللَّهَ يَجِدِ اللَّهَ غَفُوراً رَّحِيماً} [النساء:110].
((إِلَّا مَن ظَلَمَ ثُمَّ بَدَّلَ حُسْناً بَعْدَ سُوءٍ فَإِنِّي غَفُورٌ رَّحِيمٌ )) (11: النمل).
(( فَمَن تَابَ مِن بَعْدِ ظُلْمِهِ وَأَصْلَحَ فَإِنَّ اللّهَ يَتُوبُ عَلَيْهِ إِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَحِيمٌ)) (المائدة:39).

Don haka, Allah ya bude kofa gare ka ya kai dan adam mai yawan zalunci. Ka tuna duk irin nau’in jama’ar da ka zalunta. Sannan ka bi hanyar sasantawa da su tun ba a tafi lahira ba suka nemi ladarka sa’adda ka fi kome bukatuwa zuwa gare ta, kuma a rannan kana ji kana gani za a ba su ladar azuminka da umrarka da sauran ibadarka.

An gabatar da ita a ranar 2 ga jimada Akhir 1432H

HUDUBARMU TA YAU

Leave a comment

DAGA MASALLACIN ABU HURAIRA (RA), SOKOTO.

Yau Jum’ah 19 ga Safar 1433H wadda ta yi daidai da 13 ga Janairu 2012 Sheikh Muhammad Sani Abdullahi Na’ibin liman na farko ya jagoranci sallah a wannan masalaci.
Sheikh ya gabatar da huduba mai kama jiki a kan hanyoyin da musulunci ya bi wajen magance matsalolin da yan Adam ke fama da su.
Sheikh ya fadi cewa, babbar matsalar al’umma wadda mutane ba su mayar da hankali gare ta ita ce ta rashin akida; rashin sanin cewa Allah yana tare da kai, yana kallon aikinka, kuma zaka koma zuwa gare shi ya yi ma sakayya a kan aikinka.
Bayan da Sheikh ya jero matsaloli masu dama tare da bayanin wada musulunci ka magance su sai ya yi magana a kan zaluncin da ake yi a wannan kasa. Maganar cire tallafin Mai kamar yadda ya ce zalunci ce zalla da take nuna rashin tausayin shugabanni ga talakawa. Domin kuwa in muka dubi irin yadda suke cika su batse a cikin dukiyar gwamnati to, zamu ji tausayin kanmu a ce dan tallafin ma da muke moriya da shi zai tsone masu ido. Don haka ya yi kira da su ji tsoron Allah su kuma dubi talakawa da idon rahama.
Sannan ya ce, mu waiwayi kanmu mu gani, mu ma zalunci yana nan dabaibaye da mu. Misali, a lokacin da aka ba da sanarwar cire wannan tallafi ba wani gidan mai na musulmi da ya yi tunanin cewa sauran Wanda Nike da shi na saye shi ne da tallafi don haka bari in ci gaba da sayar da shi a haka har ya kare. Don haka, ya ce mu ji tsoron Allah mu yi wa kanmu adalci don mu samu adalci daga bangaren shugabanni.
Zamu kawo maku wata huduba cikakkiya da muka yi can baya kafin wannan matsala a ranar Jum’ah 2 ga Jimada Akhir na shekarar bara. Taken hudubar shi ne HADARIN ZALUNCI.
Ku dakace mu.

ALBARKA DA YADDA AKE SAMUN TA

1 Comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Abu ne mai kyau mu yi tunani a kan sa, yadda Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya hore ma mutanen wannan zamani hanyoyin jin dadin rayuwa iri-iri, tun daga yawan hanyoyin sufuri da na sadarwa da na’urorin sanyaya dakuna ko dumama su, da na dumama abinci da kawata gidaje da ado ga tituna da hasken lantarki da dai sauran su. Kome ya zama mai sauki a wannan zamani; isar da sako ake yi a cikin kyaftawa da bismillah, a samar da abinci mai dadi ta hanyar girki da na’ura mai amfani da Gas maimakon itace, a karanta kuma a duba labarai a sadda suke faruwa kome nisan wuri a cikin duniyar nan, a kuma karanta littafan ilimi kowane iri a cikin kwamfuta da hanyar gizagizan Intanet. Abincin da muke ci a yau ya fi na mutanen da dadi da inganci da lafiya. Karatunmu da wayewarmu sun fi na uwayenmu yawa da fadi. A da, sakesaki kawai iyayenmu suka sani. A yau nau’oin magunguna ba su kirguwa. Dubi yawan kasuwanni da gidaje da tituna da ababen hawa da na’urorin sadarwa da dai sauransu, za ka san irin ni’imomin Allah da muke ciki a wannan zamani. Amma kuma duk da haka, mai hankali da nazari idan ya duba da idon basira zai gano cewa, mutanen da sun fi mu jin dadin rayuwa. Sun fi mu ni’imtuwa da kasancewa a cikin kwanciyar hankali. Ga karancin curuta da kyakkyawar zamantakewa a tsakanin su. Mene ne sirrin wannan abu? Me ya sa muka fi su yawan ilmoma da tarin littafai da hanyoyin bincike amma suka fi mu gane gaskiya? Me ya sa muka fi su hanyoyin kusantar juna amma muka fi su nisantar juna? Muka fi su tattalin arziki amma suka fi mu wadata? Amsar wannan tambaya ita ce, Albarka. Akwai albarka mai tarin yawa a rayuwarsu da iliminsu da sana’arsu wadda ita ce aka rasa a tamu rayuwa da sana’a da ilimi.

Wannan maganar gaskiya ce da ba ta da tambaba. Mu yi la’akari da adadin sahabban manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Duk ba su kai yawan wata karamar hukuma a Najeriya ba amma sun canja alkiblar duniya gaba daya, sun gusar da duk turakun zalunci suka kafa adalci, sun kawar da duhu da hasken shiriyar alkur’ani da Hadisi. A cikin tarihin wannan kasa abin ya maimaitu kamar yadda ya maimaitu a kowadanne irin kasashe. Dubi yawan almajiran mujaddidi da mataimakansa. Kai dubi ma kayan aikin da suka yi amfani da su na jihadi da na kasuwanci da har na ilimi. Wasu daga cikin littafan mujaddidi Allah ya jikan sa sai an hada guda 40 kafin su yi mujalladi guda. Wani littafin ma bai wuce ka karance shi a minti ashirin ba. Da su ne ya kawar da shirka da bidi’a da zalunci a wannan kasa. Da kuma su ne ya hada rundunar mujahidai wadda ta yi awon gaba da duk azzaluman da suka taushe hakkin bayin Allah, sannan suka kafa al’umma da gwamnati bisa ga turbar Sunnah ta ma’aiki Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Wannan duka albarkacin imanin da suke da shi mai karfi da tsarkin zukatansu game da son Allah da manzo Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Wannan alkawari ne na Allah madaukakin sarki da yake cewa :

((مَنْ عَمِلَ صَالِحًا مِنْ ذَكَرٍ أَوْ أُنثَى وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَنُحْيِيَنَّهُ حَيَاةً طَيِّبَةً وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَجْرَهُمْ بِأَحْسَنِ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ)) [النحل:97]  ((وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى آمَنُوا وَاتَّقَوْا لَفَتَحْنَا عَلَيْهِمْ بَرَكَاتٍ مِنْ السَّمَاءِ وَالأَرْضِ..)) [الأعراف:96].

Hudubarmu a yau zata yin nazarin me ake ce ma albarka? Wadanne abubuwa ne ake sa ma albarka? Kuma ya ake samun ta? Ko ana gadon albarka? Me ya sa mutanen da suka fi mu ita? Kuma akwai yadda zamu yi mu same ta ko abu ce da ta riga ta wuce sai labari?

Albarka ita ce karuwar abu da wadatuwarsa da samun cikakkiyar gamsarwa a cikin sa. Idan aka ga karamin abu wanda bai cika fuska amma yana biyan muradi akan ce wannan abu yana da albarka. Misalin wannan abinci da muke ci. A wani lokacin zaka ga abinci kankane ya wadace ka, watarana kuma sai kayi ta zubawa tunbin ba ya gamsuwa yana ta neman kari. Banbancin shi ne, abincin na farko shi ne mai albarka. Idan muka dauki wannan ma’auni sau da yawa zamu ga rayuwar mutanen kauye ta wasu fuskokin ta kan fi rayuwar ‘yan birni albarka, rayuwar wani talakka ta kan fi ta wani mawadaci albarka.

Albarka ta Allah ce. Kuma duk abinda yake da alaka da Allah to, lalle ne zai yi albarka. Wanda ba ya tare da allah kuma lalle ne zai rasa albarka.

((وَتَبَارَكَ الَّذِى لَهُ مُلْكُ السَّمَـاواتِ وَالأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا وَعِندَهُ عِلْمُ السَّاعَةِ وَإِلَيْهِ تُرْجَعُونَ)) [الزخرف:85].

Duk in da albarka ta shiga ga abinda yake kalilan ne sai ya yawaita, in yana da yawa sai ya zan mai amfani. Don haka, albarkar rayuwa ba ita ce yawan shekaru ba. Albarkar kudi kuma ba ita ce tulin Naira ba. Kowa na da bukatar albarkatun ubangiji kamar yadda annabin Allah Dawud Alaihis Salam ya ce ma Allah a lokacin day a rinka kwasar fari na zinari da Allah ya saukar, sai Allah ya ce ma sa: “Haba Dawud! Ashe ban ba ka abinda ya fi wannan ba?” Sai ya ce, haka ne ya ubangiji na rantse da girmanka. Amma ba ni iya wadatuwa daga albarkokinka. Wannan shi ya sa manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya kasance yana rokon Allah ya sa ma sa albarka ga duk abinda ya ba shi kamar yadda ya ce a hadisin kunuti da ke cikin Sunan na Tirmidhi.

Allah ya kan sa ma annabawa albarka ga da’awarsu, kamar yadda ya albarkaci annabi Isah Alaihis Salam:    وَجَعَلَنِى مُبَارَكًا أَيْنَ مَا كُنتُ وَأَوْصَانِى بِالصَّلَواةِ وَالزَّكَواةِ مَا دُمْتُ حَيًّا [مريم:31].

Ya kuma ce ma Nuhu Alaihis Salam: قِيلَ يانُوحُ اهْبِطْ بِسَلَـامٍ مّنَّا وَبَركَـاتٍ عَلَيْكَ وَعَلَىا أُمَمٍ مّمَّن مَّعَكَ [هود:48].

Shi kansa ma annabi Nuhu Alaihis Salam da zai nemi masauki mai albarka ya nema:

وَقُل رَّبّ أَنزِلْنِى مُنزَلاً مُّبَارَكًا وَأَنتَ خَيْرُ الْمُنزِلِينَ [المؤمنين:29].

Annabi Ibrahim Alaihis Salam da iyalansa duk Allah ya yi ma su albarka:

وَبَشَّرْنَـاهُ بِإِسْحَـاقَ نَبِيًّا مّنَ الصَّـالِحِينَ وَبَـارَكْنَا عَلَيْهِ وَعَلَى إِسْحَـاقَ [الصافات:112، 113]

رَحْمَتُ اللَّهِ وَبَرَكَـاتُهُ عَلَيْكُمْ أَهْلَ الْبَيْتِ إِنَّهُ حَمِيدٌ مَّجِيدٌ [هود:73].

Malam Ibnul Kayyim ya ce: Duk a tarihin duniya ba wani gida da Allah ya yi ma albarka kamar wannan gidan na Annabi Ibrahim Alaihis Salam domin babu wani mutum da zai shiga aljanna tun daga zamaninsu har zuwa tashin alkiyama face sai ya bi ta hanyarsu domin ba wani annabin da Allah ya taba aikowa bayan Ibrahimu Alaihis Salam sai fa daga zuri’arsa.

Alkur’ani littafi ne mai albarka, mai yawan alhairai da waraka ga curotocin mutane.         وَهَذَا ذِكْرٌ مُّبَارَكٌ أَنزَلْنَـاهُ [الأنبياء:50]

Kamar yadda Suratul Bakarati take sura mai albarka kamar yadda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce a cikin hadisin Imamu Ahmad. Daga cikin albarkokinta ne kuma wanda ke karanta ta yake gagarar matsibbata.

Daga cikin manyan abubuwan da ke sa albarka ga rayuwa akwai sada zumunci da biyayya ga mahaifa. Albarkar aure ita kuma tana samuwa ne idan an bi ka’idojin Shari’ah, an kauce ma barna, an kuma sawwaka ma juna. Macce mai albarka ita ce mai da’a ga Allah da biyayya ga mijinta. Da mai albarka shi ne mai amfanin mutane. Duk aikin da aka fara shi da sunan Allah zai yi albarka. Haka duk cinikin da aka yi shi ba yaudara ba karya babu algussu shi ma Allah zai sa ma sa albarka. Dukiya mai albarka ita ce wadda ake amfanar da mutane da ita idan ya kasance an samo ta ne ta halal. Dan kasuwa mai cin riba kadan don ya sawwaka ma mutane ya fi samun albarka a kan mai tsanantawa. Koshin zucci godiyar Allah a kullum suna janyo albarka da karuwar abu.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce: « Dukiya ba ta taba ragewa don sadaka ba. Kuma Allah bai taba kara ma mai yin afuwa ga dan uwansa kome ba sai karin girma. Sannan babu wanda ke yin tawali’u don Allah sai Allah ya daukaka shi ».

Wuraren zama masu albarka su ne wadanda ake ambaton Allah ko aikata wasu ayyukan da’ar Allah a cikin su. Shi ya sa mala’iku ma suna zuwa wadannan wuraren ayi da su kuma suyi ma mummunai addu’a. Lokaci mai albarka shi ne wanda ya tafi alhalin mutum na cikin amfanuwa da shi, bai daukar ma kansa kowane irin zunubi a cikin sa ba. Sallama da muke yi ma juna idan mun hadu ko in zamu shiga gida tana kawo albarka. A duk lokacin da mutum ya fi zama kusa da Allah to, lokacinsa ya fi albarka. Duba yadda sayyidina Abubakar a safiya guda ya ci da talaka, ya je duba maras lafiya, ya halarci jana’iza kuma ga shi yana azumi. Kuma manzon AllahSallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma sa, duk wanda ya hada su a rana daya zai shiga aljanna. Muslim ya ruwaito shi.

Idan mutum ya yi aure ana son a rokar ma sa albarka, haka ma idan ya samu haifuwa ko ya kama aiki ko ya fara gina gida ko zai yi tafiya ko zai fara karatu ko duk wani al’amari na rayuwa.

Mutum da kansa zai nemi albarka ga al’amurran rayuwarsa ta hanyar kiyaye dokokin da aka sa sai ya same ta. Idan zaka ci abinci ka yi bismillah kuma ka ci a gabanka zaka samu albarka. Haka ma in ka gama cin abinci ka sude yatsunka zaka samu albarka. Cin abinci a cikin jama’a shi ma yana sa albarka kamar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma Wahshiyyu dan Harbu a lokacin da ya koka cewa, suna cin abinci ba su koshi, sai manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya ce ma sa: « Hala kuna ci daban daban ne? » sai ya ce, eh. Ya ce, « To, ku rinka haduwa ku ci tare, kuma ku fara da sunan Allah sai a sa ma ku albarka ».

Ruwan da ya fi kowane amfani da albarka shi ne Zamzam. Garin da ya fi albarka shi ne Makka sannan Madinar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Sallah a masallacin Makka ta fi ninkin lada fiye da sau dubu dari a wani wuri ba can ba. A masallacin Madina kuma ta fi sallah dubu idan ba a can ne ba. A cikin gidaje, gida mafi albarka shi ne dakin Allah da ke Makkah:

إِنَّ أَوَّلَ بَيْتٍ وُضِعَ لِلنَّاسِ لَلَّذِى بِبَكَّةَ مُبَارَكًا وَهُدًى لّلْعَـالَمِينَ [آل عمران:96].

Madina kome nata mai albarka ne saboda addu’ar manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama. Bayan Makka da Madina babu wani gari da ya kai albarkar Sham wadda Allah Ta’ala ya kira ta mai albarka a wurare hudu cikin alkur’ani. A cikin ranaikun mako Allah ya fi sanya albarka ga ranar jum’ah, a ranaikun shekara kuma ranar Arafat, a dararen shekara kuma Lailatul Kadari. A cikin watanni kuma Allah ya fifita Ramadhana da karin albarka. Haka kuma manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallama ya roki Allah ya sa albarka ga duk abinda aka yi saukon yin sa a cikin al’ummarsa. Wannan shi ya sa tafiyar safe da aikin safe da karatun safe da komai wanda aka yi sammako a cikinsa yake da albarka. Kuma don muhimmancin wannan lokacin ne Allah Ta’ala ya yi rantsuwa da shi a suratut Takwir (Aya ta 18).

Ya ku bayin Allah! Duk wuraren da ake bayyana da’ar Allah babu shakka albarkatun ubangiji sukan bayyana a cikin su. Haka kuma duk in da ake bayyana sabon Allah da kangara to, lalle ne a ga rashin albarka a wannan wurin. Allah Ta’ala ya yi gaskiya da yake cewa:

((وَلَوْ أَنَّ أَهْلَ الْقُرَى ءامَنُواْ وَاتَّقَوْاْ لَفَتَحْنَا عَلَيْهِم بَرَكَـاتٍ مّنَ السَّمَاء وَالأرْضِ وَلَـاكِن كَذَّبُواْ فَأَخَذْنَـاهُمْ بِمَا كَانُواْ يَكْسِبُونَ)) [الأعراف:96].

Ya ku ‘yan uwa musulmi! Mu nisanci abubuwan da ke shafe albarka wadanda suka hada da saba ma Allah a cikin kowane irin sha’ani. A cikin ciniki misali rantsuwar karya da yaudara na shafe albarka. A sha’anin hulda ta kudi cin riba ko bayar da ita na shafe albarka. Haka ma rowa ga wanda Allah ya wadata tana shafe albarkar kudin da mai kudin baki daya. Neman abinci ta hanyar roko ko bara ko damfara ko sata duk suna shafe albarka. Mu nisance su. Babu dukiyar da ke albarka ta zamo mai cikakken amfani in ba wadda nema ta hanya shar’antacciya ba. Idan kuma an samu a gode ma Allah; kada a yawaita dogon guri domin shi ma yana shafe albarka.

Ya Allah! Muna rokon ka da sunayenka kyawawa da siffofinka madaukaka, ka sanya albarka ga rayuwarmu da ayyukanmu da iyayenmu da iyalanmu da zuri’armu. Ya Allah ka ba mu dukiya mai albarka, ka zaunar da mu lafiya a cikin kasarmu, ka shugabantar da mutanen kirki a kan mu. Ka dauke mana jarrabawar shugabanni barayi, azzalumai, mayaudara.

Ya Allah! Ka azurta mu da ruwa masu yawa da albarka, ka kare mu daga fari da tashin hankali da annoba da musibbu manya da kanana.

Allah ka tsarkake zukatanmu ga duk abinda mu ke aikatawa. Ka yi mana karshe mai kyau, mu gama lafiya, mu cika da imani.

An gabatar da ita a ranar jum’ah 23 ga Jimada Akhir 1432H

MANUFOFIN SHARI’AH

Leave a comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Addinin musulunci addinin Allah ne. Kuma ya dace da kowane zamani da kowane wuri da kowane yanayi. Addinin ya wuce wasa tunda halittarmu kan ta ba ayi ta don wasa ba. Suratul Mu’minun: 115-116 da kuma Suratud Dukhan: 38-39.

Babbar manufar addinin musulunci ita ce kyautata rayuwar dan adam. Duk abinda ka ga an ce ayi shi ko a bari, duk wata ibada ko wani hukunci ko doka a addinin musulunci manufarsu ita ce kyautata rayuwa domin ta zamo a kan tsarin da ya dace. Rayuwa ba ta kyautatuwa a nan duniya sai an bi addinin musulunci, haka ma gobe kiyama.

Addinin musulunci ya kalli kyautatuwar rayuwa ta fuskoki guda uku:

  1.            I.        Akwai abin da yake kyautata rayuwa kuma lalura ne don ba ta tsayuwa sai da shi
  2.          II.        Akwai wanda ake da bukata da shi amma bai zama dole ba
  3.       III.        Na uku shi ne abinda ado ne kawai da karin jin dadi amma rayuwa na tafiya daidai ko ba a same shi ba.

Duka wadannan addinin musulunci ya yi kyakkyawan tanadi ma musulmi game da su. Muhimman abubuwan rayuwa na lalura guda shida ne. Duk wanda aka rasa cikin su rayuwa za ta shiga wani hali na tagayyara da lalacewa ko kuma a rasa ta gaba daya. Bisa ga haka musulunci ya ba su kulawa ta musamman, ya kuma shata dokoki domin tabbatar da ingancin su. Wadannan abubuwa su ne:

1. Addini

2. Rayuwa ita kan ta

3. Mutunci wanda mutum ya kebanta da shi

4. Hankali, wanda ya raba dan adam da dabba

5. Zuri’a, ma’ana ci gaba da haifuwa don wanzuwar mutane kada su kare

6. Dukiya, abokiyar tafiyar rayuwa

Wadannan abubuwa guda shida kowanne muka dauka zamu ga addinin musulunci ya yi masa tanadi iri biyu; na farko yadda za a samar da shi, na biyu yadda za a tsare shi a martaba shi.

Manufa Ta Daya: Kare Addini

Duk abinda ka sani na ci gaba a rayuwa an yi al’ummomin da ba su da shi. Misali, an yi al’ummomi da yawa da ba su da ilimi, ba su karatu da rubuta, ba su da wayewa, ba su da ci gaba kowane iri amma ba a taba samun wata al’ummar da ba ta da addini ba. Wannan shi zai nuna mana muhimmancin addini ga rayuwa. Musulunci ya sanya addini a matsayin lalura ta farko ga rayuwar dan adam. Suratur Rum: 30.

Ga kuma wasu matakan da ya dauka don karfafa samuwar sa da ba shi kariya.

a. Musulunci ya ginu a kan shikashikai guda biyar wadanda na farkonsu shi ne tauhidi wanda ya ke sanar da mutum mahaliccinsa da siffofinsa wadanda za su sa ya san girmansa. Ya kuma kunshi sanin manzanni da sakon da suka zo shi. Sauran shikashikan kuma sun hada da ibadodi da suke gyara alaka tsakanin mutum da mahaliccinsa da kuma tsakaninsa da jama’a.

b. Domin mutum ya san Allah an karfafa masa duba zuwa ga halittu. An ce ya yi tunani kada ya dogara ga “mun isko iyaye” kada kuma ya koyi wasu. A’a, dole ne ya yi aiki da hankalinsa. Suratul Bakarah: 170.

  1. Addinin musulunci ya wajabta kira da yin wa’azi zuwa ga addini da karantar da mutane gaskiya. Don haka dole ne a kowane lokaci a samu masu karantar da addini. Suratu Ali Imran: 104

Wadannan duka matakai ne da aka dauka don samar da addini da yaduwar sa a tsakanin mutane. Haka ma bayan samuwar addinin an dauki matakai don ci gaban sa da kariyar sa kamar haka :

a. Dole ne a bar kowa da ‘yancinsa kada a tilasta shi bin addinin da bai gamsu da shi ba. Suratul Bakarah: 256

b. Sai kuma shar’anta jihadi wanda aka yi shi don samar ma mutane ‘yanci ba don tilasta su su bi addini ba. Suratul Hajji: 40 da Suratun Nisa’i: 75.

  1. Domin kada ayi wasa da addini sai aka sanya hukuncin kisa ga wanda ya yi ridda daga addinin musulunci don kar a mayar da shi abin izgili kamar yadda wasu suka yi. Kuma don mutum ya yi kyakkyawan nazari ba zai shiga addini ba sai bayan ya gamsu sosai da kyawonsa, sai ya yi shi don Allah ba don neman wata bukatar duniya ba.

d. Akwai kuma wasu abubuwa masu dinbin yawa da aka sa don karfafa musulunci a cikin zukata kamar sa ayi sallah cikin jama’a, da kwadaitarwa ga yin nafiloli na azumi da sallah da sadaka da dai sauran su.

Manufa ta Biyu: Tsare Rayuwa

Addinin musulunci ya kula da rayuwar dan adam ta kowace fuska. Misali, ya wajabta dan adam shi kansa ya tsare rayuwarsa. Dole ne ya ci abinci, ya sha ruwa, ya nemi wurin kwana inda sanyi ko zafi ba zai kashe shi ba. Akwai lokutta da shari’ar musulunci take tilasta ma mutum ya ci abinci ko da ta kai ga sai ya yi kwace ne don dai ya tsare rayuwarsa kada ya mutu. Haka kuma an wajabta masa nisantar duk abinda zai iya halakar da rayuwarsa in ba bisa ga umurnin shari’a ba. Sannan dole ne ya kare rayuwarsa daga duk wata barazanar kisa daga ‘yan fashi ko ‘yan ta’adda har ma in ya mutu wajen wannan fafutukar ya yi shahada. Mu dubi ko a cikin ibada yadda addinin musulunci ya ke ta kaffa-kaffa da rayuwar dan adam; ana ta samar masa sauki idan ya yi tafiya ko in ba ya da lafiya ko in ana ruwan sama da makamantan su. Suratul Ma’ida: 6 da Suratul Hajji: 78.

Sannan musulunci ya wajabta ma mahukunta su samar da tsaro da kwanciyar hankali ga jama’a, su hukunta duk wanda zai kawo ma tsaro cikas a cikin jama’a. Daga nan ne ya wajaba a samu ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da na bincike da leken asiri, a kuma samu kotuna da alkalai da rubutattun dokoki wadanda ake tsamo su daga cikin shari’a wadanda kuma su zasu jagoranci alkalai su hana su kauce ma hanya da cin zalun.

Bayan haka sai addinin musulunci ya haramta kisan kai, ya tsananta hukuncinsa har ma wanda ya kashe rai guda kamar ya kashe rayuwakan bil adama baki daya, kuma hukuncinsa shi ne Jahannama khalidan fi ha. Suratun Nisa’i: 93.

Sannan musulunci ya wajabta kisasi da kuma diyya, ga kuma kaffara saboda hakkokan da suka rataya na ‘ya’yan wanda aka kashe da danginsa da kuma hakkin ubangijin da ya halicce shi. Shi kuma wanda aka kashen nasa alhaki sai lahira ya jawo wanda ya kashe shi ya gurfanar da shi gaban Allah yana neman abinsa. Haka kuma yana daga cikin dokokin musulunci wajabcin kubutar da duk wanda aka ga za a kashe shi bisa ga zalunci ko da kafiri ne. Musulunci bai yarda a kashe kowa ba sai bisa ga dalili karbabbe cikin shari’a. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce: Duk wanda ya kashe kafirin amana ba zai ji kanshin aljanna ba – saboda nisan sa da ita – duk da yake ana jin kanshinta tun ana nesa da ita; tafiyar shekara 40. (Sahihul Bukhari, Hadisi na 2995).

Manufa Ta Uku: Tsaron Mutunci

Ba kowace irin rayuwa ce addinin musulunci yake son mu yi ba sai dai nagartacciyya wadda ta dace da mutuntaka da Allah ya daukake mu da ita. Suratul Isra’i: 70.

Don haka ne Allah ya ba mu ‘yanci na tunani da zabin addini, ya mallaka mana ababe da ya hana ayi jayayya da mu cikin su kamar kasar da muke rayuwa da makamancin haka. Sannan ya umurce mu da tsare mutuncin juna. Aka hana kazafi da zagi da sukar lamiri. Kuma duk wanda ya yi ma wani daya daga cikin wadannan to, take zai gamu da fushin shari’a. akwai kuma dokoki da suke hana shiga gidan wani ba da izninsa ba, ko leke daga waje duk dai don kariya ga mutuncinsa.

Manufa Ta Hudu: Tsaron Hankali

Hankali shi ne kadaitaccen abinda dan adam ya tsere ma sauran halittu na tudu da na teku da shi. Wasu halittu sun fi dan adam karfi da ginin jiki da cin abinci da yawan haifuwa da tsawon rayuwa da komai, amma duk ya fi su hankali da dabara. Don haka ne ma ba irin halittar da bai kiwo amma shi babu mai kiwon sa. Wannan shi ya sa ya kai matsayin a ba shi rikon amana irin wadda sama da kasa da duwatsu suka ji tsoron dauka.

Don haka addinin musulunci ya haramta ci ko sha ko shakar duk wani abinda yake gurgunta hankali ko ya gusar da shi. Kuma ya sanya dokoki masu tsanani a kan wanda ya saba wannan umurni. Addinin musulunci ya yi umurni da duk abinda zai karfafa hankali. Shi ya sa ya ce a nemi ilimi. Kuma ya yarda da duk wani halattaccen abinci wanda ke karfafa kwakwalwa. Sannan ba a yarda mutum ya zauna da yunwa ba har wadda zata cuta ma hankalinsa. Dokokin musulunci ma ba a yarda alkali ya zartar da su ba in yana jin yunwa. Kuma idan aka kawo abinci lokacin sallah ya yi to, shari’a ta ce a fara cin abinci don hankali ya tattara wuri guda ayi ibada cikin natsuwa.

Daga cikin ba hankali kariya shari’ar musulunci ta hana tsibbace-tsibbace da duba da bokanci saboda abinda suke tattare da shi na karya da shu’umci da yaudara da bata hankali da wuce gona da iri. Kuma addini ya hana mutum ya shigar da hankalinsa inda bai dace ba. A maimakon haka shari’ar musulunci tayi tanadin wasu hanyoyi da suke amfanin hankali su kaifafa basira su zazafa tunani. Misali yin nazari game da halittu da nazarin alkur’ani don fitowa da asirransa da kokarin gano hukunce-hukuncen shari’a musamman ga sababbin lamurra wadanda suke faruwa.

Manufa Ta Biyar: Kariyar Jinsin Dan Adam Daga Karewa

Yana daga cikin manufofin addinin musulunci samar da lafiyayyar hanya ta ci gaban jinsin dan adam da hana shi karewa har zuwa lokacin da Allah zai yi ikonsa; ya nade tabarmar kasa da wadanda ke cikin ta. A kan haka ne Allah Ta’ala ya shar’anta aure, ya dora ma iyaye kula da rayuwar ‘ya’yansu da daukar nauyinsu tare da lura da kulawa da tarbiyyarsu har zuwa sadda zasu wadatu daga haka. Kuma sai aka sanya wasu dokoki wadanda suke hana ma aure ci gaba. Don haka aka haramta zina da duk abubuwan da ke sa a kai gare ta kamar bayyanar tsiraici da cuduwar jinsi da makamantan su. Addinin musulunci ya dauki zina a matsayin wani babban ta’addanci ga hakken dan adam da shiga cikin hurumin da bai mallaka ba. Don haka sai aka sanya horo mai tsanani wanda har ya kan kai ga mutum ya rasa ransa idan ya yi wannan laifin alhalin ya taba sanin dadin aure.

Manufa Ta Shida: Kariyar Dukiya

Allah ya halicci dan adam da son mallakar abin kansa. Tun daga kuruciya masu nazari na gane wannan. Addinin musu lunci bai ci karo da dabi’ar dan adam ba, sai ya bada damar mallaka ga kowane memba na jama’a ya kebanta da abinda ya mallaka ba tare da kowa ya yi masa shisshigi a ciki ba. Amma kuma idan aka kyale dan adam zai wuce nasa haddi ya shiga alhakin wasu. Don haka sai Allah Ta’ala ya sanya wasu dokoki masu sa masa linzami. Aka fadi yadda zai nemi dukiya da yadda zai sarrafa ta da juya ta. Halal da haram a babin ciniki da sauran huldodi irin bashi da kwadago da kwangila da jingina da sabtu da hannun jari da makamantansu sun fi yawa a kan sauran babobi. Kai aya mafi tsawo ma a cikin alkur’ani ita ce wadda ta yi maganar kudi « Ayar bashi ».

Addinin musulunci ya karfafa neman arziki (Abinda alkur’ani ya kira shi “neman falalar Allah ») har an dauke shi a matsayin ibada wadda ake ba mutum lada a kan ta idan ya tsarkake niyyarsa. Suratul Mulk: 15 da Suratul Jum’ah: 10.

Masu neman abinci kuma musulunci ya karimta aikinsu; ya nemi a biya su tun suna da sauran gumi a jikinsu. Duk wata hanyar da za ta cuta ma wani shari’ar musulunci ta hana neman arziki da ita. Kamar sata da zamba da caca da bashi da ruwa da makamantansu. Suratul Bakarah: 188.

Har wayau dai addinin musulunci ya hana a kimshe dukiya ko a tozarta ta ta hanyar sarrafa ta ba inda ya dace ba ko yin almubazzaranci a inda ya dace a takaita. Ya kuma yi umurni da a kula da dukiyar marayu har su girma da ta safihi wanda bai iya juya ta, ya ce kuma kada a ajiye dukiyarsu ba yaduwa, a’a ayi kasuwanci da ita don ta ci gaba.

Ya ku al’ummar musulmi! Me ya kai kyawon addininmu inda zamu tsaya mu fahimce shi; mu karance shi cikin tsanaki, mu yi aiki da shari’arsa sannan mu gwada ma duniya a aikace ga yadda addininmu ya ke. Wajibin al’ummar musulmi ne ta zamo jagora ga sauran duniya don haka ubangiji ya ke so gare mu. Suratu Ali Imran: 110.

An gabatar da ita a ranar jum’ah 11 ga Muharram 1432H (17/12/2010)

TAFARKIN MAGABATA

1 Comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Mu sani babu wata ni’ima da Allah ya yi mana wadda take gaba da kammala muna addini da ya yi, ya samar muna da godabe mikakke wanda babu karkata a cikin sa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam shi ne farkon wanda ya hau wannan godabe kuma ya bamu tabbacin tsaran sa zuwa karni uku zasu tafi kan wannan godabe, kuma ya ce muyi koyi da su, sannan ya hane mu daga bin duk hanyoyin da suka karkace ma nasu. Don haka yake da kyau a kullum mu rinka dubi zuwa ga inda suka bi don muyi koyi da su. Wannan huduba zata kara bada haske a kan rayuwar magabata Salaf wajen aiki da shari’a.

1. Magabata, musulmin farko suna girmama nassin Alkur’ani da Hadisi, kuma suna gabatar da su a kan komi. Babu wata maganar da ta kai girman maganar Allah da ta manzo a wurin su.

  • Sayyidina Abdullahi dan Abbas Radiyallahu Anhu yana cewa: Mutane zasu halaka in aka ce musu Allah ya ce, suka rinka cewa to, ai Abubakar da Umar sun ce..
  • Sarkin malaman karni na biyu Sa’id bin al Musayyib ya hana wani yin nafiloli bayan sallar asuba, sai mutumin ya ce, to, halan Allah zai azabta ni ne don nayi sallah? Ya ce, a’a. Zai dai azabtaka don ka saba ma sunna.
  • Wani kuma ya yi fatawa wurin Imamu Malik a kan yana son ya yi haramar aikin hajji daga wurin kabarin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Sai Imamu Malik ya ce masa, ka dai yi harama in da Manzon Allah ya yi. Sai ya ce: To, don mil guda da na kara? Imam ya ce masa: Ka shiga uku in ka shiga gaban Manzon Allah da mil guda!
  • Imamus Shafi’i kuma ya karanta wani hadisi sai almajirinsa malam Humaidi ya tambaye shi: kana aiki da wannan hadisi? Sai ya ce: ka ga na fito ne daga coci? Cewa zaka yi, shin ya inganta? Wane musulmi ne ke barin hadisi in ya inganta?
  • Imamus Sauri yana cewa: in kana da iko kar ka sosa kan ka sai da nassi.

2. Magabata suna tantance magana, basu karbar ta sai in ta inganta.

  • Imamu Malik yana cewa: Wannan addini shi ne jinin ka da tsokar ka. Don haka ka duba wurin wa kake daukar karatun addinin ka?
  • Ibnu Taimiyyah ya ce: An ruwaito Annabi Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce: “Za a yi mini karya”. Idan wannan hadisi gaskiya ne, ya wajaba mu yi hattara. In ko karya ne to, an fara kenan! Don haka bai halatta mu kafa hujja da wata Magana da aka jingina ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam sai mun tabbatar da ingancin ta.

3. Magabata suna tantance hakikanin ma’anar nassi kafin su kafa hujja ko su yi aiki da shi. A nan suna da wasu hanyoyi da suka dogara gare su:

  • Dole ne wanda zai bayyana ma’anar nassi ya iya gano salon harshen da nassin ke magana da shi. Ma’ana, dole ne ya kware wajen sanin larabci da yadda ake sarrafa shi.
  • Kafin a kafa hujja da nassi sai an tara ire-iren sa wuri guda an hada hancin su. Domin maganar Allah da ta manzonsa ba su warware juna.
  • Dole ne fassarar nassi ta dace da ruhin shari’ar musulunci da manyan manufofin da madaukakin sarki ya sabkar da addini domin su. Shi ne samar da rahama da adalci da maslaha ga mutane. Duk wata fassara ta nassi idan ta fita daga wannan layi to, ba hanyar magabata ce ba.

Ya ku ‘yan’uwa musulmi! Mu kula da bin magabata don su ke bisa hanyar kwarai. Mu kauce ma irin hanyoyin wadanda ke maida nassin Alkur’ani da karantarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam a baya, ko su yi wasa da su, ko su basu ma’ana bisa ga son zuciya da biyan wasu bukatu, ko su dauki addininsu daga wani wuri ba wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallamba, ba kuma wurin masu koyi da shi ba.

Babbar alamar da ke nuna cewa, mutum ba shi bisa ga Sunna ita ce ya kauce ma hanyar magabata. Idan haka ta faru dole ne daya daga cikin wadannan abubuwa ko kuma dukan su su faru:

1. Ko dai ka ga ba shi ganin girman maganar Allah da Manzo. Irin wannan ko ya kafa hujja ba ita yake bi ba, ita yake jawowa ta bi shi.

2. Ko ya rinka wasa da nassoshi, ta hanyar tawili da son zuciya.

3. Ko ya yi kokarin hada fada da tada rikici a tsakanin su; ya ce wannan nassi ya saba ma wancan, don ya dau wanda ran sa ke sha’awa.

4. Ko kuma ya kago wata karya ya jingina ma Allah da Manzon sa.

An gabatar da ita a ranar jumu’a 5TH Dhul Ki’ida 1430H

AL WALA’U WAL BARA’U

2 Comments

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Hudubarmu ta yau tana magana ne a kan wasu akidu guda biyu na musulunci da ake kira Wala’a da Bara’a.Wala’a na nufin son wanda Allah ke son a so, Bara’a kuma tana nufin kin wanda Allah ke son a ki. Abinda aka sani ga mumini shi ne yana son Allah, yana kuma son masoyan Allah; yana kaunar su, yana taimakon su. Haka kuma yana kin duk abin da Allah ke ki da wadanda Allah ke ki da duk wata dabi’a ko aikin da Allah ke ki. Don haka ne Allah ya sifaita su da cewa, ba su tsoron zargin masu zargi a kan sha’anin Allah. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya sanya wannan akida a matsayin matakin koli na imani:

( أوثق عرى الإيمان الموالاة في الله والمعاداة في الله والحب في الله والبغض في الله )

Albani ya inganta shi a cikin Silsilah Sahiha (4/306).

Idan ka ce don me zamu ki kafirai? Amsa ita ce, don su makiyan Allah ne. Kuma mu ma makiyanmu ne. Wannan shi ne abinda Allah ya fada mana a Suratul Mumtahanah:1-2 da kuma Suratu Ali Imran:28.

Wadanda Allah ke so mataki mataki ne, haka su ma wadanda Allah ke ki. Kuma wajibi ne kowa mu ajiye shi a kan matakinsa. Annabawa da manzanni suna sama ga sauran mummunai mutanen kirki. Su kuma mutanen kwarai sun tsere ma masu fajirci koda musulmi ne. Fajirai musulmi sun fi matsayi a wurin Allah da masoyan Allah a kan kafiri kowane iri.

Allah ya kira kafirai najasa. Suratut Taubah: 28.

Ya ce su azzalumai ne. Suratul Bakarah: 254.

Sannan mayaudara ne, ba su cika ma musulmi alkawali. Suratut Taubah: 1-10.

Kuma a kullun cikin kashe kudi su ke don su gurgunta addinin Allah, su ga bayansa. Suratul Furkan: 55 da kuma Suratul Anfal: 36

Kuma suna muguwar fata gare mu cewa mu kafirta irin su. Kuma zasu yi duk iya abinda zasu iya don cimma wanna kazamar manufa tasu. Suratun Nisa’i: 89, da Suratul Bakarah: 109 da 218.

Allah Ta’ala kuma ya ce, su ba su kaunar mu koda mun kaunace su sai dai su yi mana kissa, a cikin haka kuma suna kulle-kulle don ganin sun ruguza al’amarinmu. Suratu Ali Imran: 118-120.

Mu yi tunanin abinda Allah ya fada game da Banu Isra’ila cewa, rashin imani ne ya sa su son makiyan Allah. Suratul Ma’ida: 80-81.

Madaukakin sarki ya katse duk wani hanzari da musulmi zai bayar wanda yake sa ya jibinci wani kafiri makiyin Allah. Ga abinda ya ce a cikin Suratul Ma’ida:

Ya ku wadanda suka yi imani! Kada ku riki Yahudu da Kirista a matsayin masoya. Sashensu na kaunar sashe. Kuma duk wanda ya jibince su cikinku to fa hakika yana cikin su. Tabbas, Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai. Zaka ga masu ciwo a cikin zukatansu suna gaggawar shiga cikin su, suna cewa muna tsoron matsala ta same mu. To, ai Allah ya kusa ya kawo nasara ko kuma wani al’amari daga wurinsa sai su wayi gari suna masu da-na-sani a kan abinda suka boye a cikin zukatansu. Suratul Ma’ida: 52.

Haka kuma Allah ya hane mu mu kaunace su kome karfin dangartakar mu da su:

Ba zaka samu wasu mutane da suka yi imani da Allah da ranar lahira ba suna soyayya da wanda ya ki Allah da manzonsa koda kuwa ubannensu ne ko ‘yan uwansu ko danginsu. Wadancan su ne wadanda Allah ya rubuta imani a cikin zukatansu kuma ya karfafa su da wani Ruhi daga wurinsa kuma yana shigar da su gidajen aljannar da koramu ke gudana a cikinsu suna masu dawwama a cikin su. Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da Allah. Wadancan su ne rundunar Allah. Ku saurara! Hakika, rundunar Allah su ne masu rabauta. Suratul Mujadilah: 22.

Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam sun tarbiyyantu a kan wadannan ayoyi da muka karanta shi ya sa rayuwarsu ta zamo tsantsa saboda Allah. Kuma duk wanda ke kin Allah to, sun kama gaba da shi kenan ila yaumil kiyamati. Tarihi ya tabbatar da wannan. A ranar Badar misali, Sayyidina Abubakar Siddik ya kira dansa na cikinsa don su yi mubaraza, kuma ya ce da ya fito tabbas da na kashe makiyin Allah. Amru bin al Ass shi kuma kawunsa ya kashe Asi bin Hisham. Su kuma Ali da Hamza sun kashe danginsu Utbatu da Shaibatu. A ranar Uhud Abu Ubaida bin Al Jarrah shi ya kashe mahaifinsa. Mus’ab bin Umair shi ya kashe kaninsa Ubaidu. A lokacin da Abdullahi dan Ubayyu ya taba mutuncin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam da kyar ya sha daga hannun dansa wanda ya tashi kashe shi ba don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya hana shi ba.

Mujaddidi Usmanu (Allah ya kara masa rahama) ya bayyana muhimmancin wannan akida inda ya wallafa wani littafi akan ta, ya sa masa suna Kitabul Amri bi muwalatil muminin wan nahyi an muwalatil kafirin. Duk ayoyin nan da muka kawo Shehu ya kafa hujja da su yana mai cewa, babu sassafci ko kadan a cikin wannan lamari. Da haka shi ma ya gina al’ummar da ta kafa daular musulunci a wannan kasa.

Ya ku al’ummar musulmi! Tarihi ya tabbatar da cewa, babu wata akida wadda ta taimaki musulmi wajen kafa addinin musulunci kamar wannan akida ta Wala’a da Bara’a. Sanin haka shi ya sa Tattar na wannan zamani suke ta kai da komo a cikin kasashen musulmi – musamman na larabawa – suna neman a cire wannan babi daga manhajar karatun yara.

Haka kuma tarihi ya tabbatar da cewa, babu sadda musulmi suka gamu da matsala ga rayuwarsu kamar lokacin da suka yi biris da wannan akida. Mu karanta labarin Muhadirud Daula, wani kirista da ya samu matsayi a zamanin gwamnatin sarki Al Malik As Salihwanda saboda irin matsayin da yake da shi da mike kafafu a kasar musulmi sai da ya kai ga sa wani kirista da ya musulunta ya koma ga addininsa. Wannan mutum ya wulakanta musulmi matuka, musamman kuma malamai. Haka kuma an ce a gidansa kullum akwai baki daga kasashen waje wadanda ba musulmi ba. Kai, daga karshe dai shi ne ya jawo Faransawa ya taimaka ma su suka ci musulmi da yaki bayan duk amincewar da musulmi suka yi ma sa. Wannan tarihi ya maimaitu a lokutta da dama. Duk sadda musulmi suka amince ma kafiri, suka kyautata ma sa zato, ko suka dauke shi wawa wanda bai san abinda yake ba, to, sai sun dandana kudarsu a hannunsa.

Wannan shi ne abinda ya faru kuma yake faruwa a wannan kasa tamu. Daga gidan kaso musulmi ‘yan arewacin kasar nan suka je suka dauko wani criminal wanda ke jiran hukuncin kisa. Suka wanke shi daga laifinsa. Suka gyara ma ‘yan Najeriya shi. Suka yi masa kanfe. Suka ba shi kudi da duk kayan aikin da yake bukata, suka maida shi shugaban wannan kasa. Ba su yi wannan don Allah ba, ba su yi don ci gaban wannan al’umma ba. Sun yi haka ne don nasu bukatun na kashin kansu. Sai Allah Ta’ala ya tabbatar da gaskiyar maganarsa. Wannan mutum ya zame ma najeriya da ‘yan najeriya kaya, musamman ma dai musulmi. Da kyar da addu’oi Allah ya gwada mana baya gare shi. Su kuma wadannan da suka yi masa wannan gata, sai ya wayi gari ba shi da makiyi; abokin gaba da adawa irin su.

To, a yau ma wancan kuskuren da wadancan suka yi shi wasu ke son su sake maimatawa. Ba zasu yi wannan don suna tunanin wani alheri ga kasa ko ‘yan kasa ba. Ba zasu yi haka don suna son zaman lafiya ko ci gaban jama’a ba. A’a, su dai suna da wasu bukatu na kashin kansu da suke son biya ta hanyar yin haka.

Wannan mutum dai tashin farko ya nuna mana ko shi wane ne. Ya fara da kwashe rijiyoyin mai guda tara na wannan kasa ya mallaka ma jaharsa. Ya wanke ‘yan uwansa daga ta’addancin da su da kansu suka yi ikirarin sun yi shi. Ya tsayar da wani kataferen project na gyara tattalin arzikin arewa wanda marigayi Umaru Musa ya basuwa. Kafin haka wannan project Gen. Abdussalami ne ya bada shi, Obasanjo ya soke. Wannan fa ba a yi zabe aka tabbatar da wannan mutumin ba kenan. To, ina ga ya kama tenure ta kansa?!

Muna tunatar da al’ummar musulmi da dukkan wadanda abin ya shafa cewa, wannan lamari fa akida ne. Kuma wanda bai ji maganar Allah ba lalle ne zai ji ta shaidan. Don haka wajibi ne ga duk wanda ke da iko ga tsayar da ‘yan takara ya tabbata ba shi da hannu ga dora kafirci a kan musulunci. Idan ta dawo tsakanin musulmi da musulmi kuma wajibi ne a kamanta neman mai dama-dama wanda ake sa ran samun gyara da ci gaba a karkashin mulkinsa. Mu nemi gyara tun yanzu don kanmu da diyanmu da suke tafe a bayanmu. Mu tuna, abubuwa ukku su ne jigon rayuwar wannan kasa: Na farko Ilmi, Na biyu arziki, Na uku shugabanci. Biyu na farko mun riga mun rasa su. Idan muka yi sakaci da ukkun to ba abinda za a ce sai La haula Wa la kuwwata illa billah.

Abinda ya faru ga wasu kasashen Afrika ya kamata ya zama darasi a gare mu. Ga Benin nan wadda a da ake kira Dahomey. Kasa ce ta musulmi da a yanzu tana son ta yi mu su kanshin dan goma. Wannan shi ne abin da ya faru a kasar Cameroon bayan kuren da Alhaji Ahmad Ahidjo ya tabka na amince ma mataimakinsa wanda Allah ya ce kada a amince ma. Halin da Ruwanda take ciki shi ma wani darasi ne. Haka Ghana da Cote d’iboire da Djibuti da sauran su. Me ya sa ma zamu je nesa? Abinda yake faruwa a Jos kawai ya ishe mu. Duk wadannan wurare da muka zana na musulmi ne tun can asali amma saboda sakaci da amince ma wadanda Allah ya ce su mayaudara ne sai ganwo ya jirkice ma dame. Saboda haka, yana da kyau mu farka tun lokacin nadama bai zo ba.

A karshe muna kira daga wannan mimbari zuwa ga duk musulmin kasar nan cewa, su yi rajista don shirin zabe wadda za a yi daga 15 zuwa 29 ga wannan wata na Janairu da muke cikin sa. Haka ma su bari duk iyalansu maza da mata wadanda suka cika shekarun da ake nema su ma su yi rajista. Domin ka’idar musulunci ita ce, yaki yana zama wajibi ga musulmi idan aka kawo hari cikin gida a kan kowa da kowa; namiji da macce ba a dauke ma kowa. A halin da muke ciki kuwa an riga an kawo mana hari har kuryar daki. Don haka dole ne mu tashi tsaye. Ya Allah! Ka taimake mu. Allah ka yi muna dace, ka dibarta mana; kada ka bar mu da dibarar kawunanmu.

An gabatar da ita a ranar juma’a 2nd Safar 1432 A.H

ME KE HANA MU TUBA?

Leave a comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Godiya ta tabbata ga Allah wanda shi ne mai gafarar zunubi, mai karbar tuba. Tsira da aminci da salati su tabbata ga Manzon Rahama Muhammadu dan Abdullahi wanda ya fi kowa tuba da kankan da kansa ga Allah sarki mai gafara.

Ya ku bayin Allah! Mummuni ba ma’asumi ne ba daga yin laifi babba ko karami. Haka kuma bai wuce ya fada cikin wani tarko ba na shedan ko wani rami na son zuciya. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce: Kowane dan adam mai yin kuskure ne, kuma mafiya alheri daga cikin masu kurakurai su ne wadanda ke tuba. (Ahmad da Tirmidhi suka ruwaito shi daga Anas Radiyallahu Anhu). Siffar Allah Tabaraka Wa Ta’ala ta kasancewar sa mai gafara da karbar tuba ba ta tabbatuwa har sai an samu masu laifi kuma suna tuba sannan ya gafarta ma su. Shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yake cewa: Hakika da ace ba ku yin zunubi da sai Allah ya tafi da ku, ya kawo wasu masu yin zunubi suna tuba sai yana gafarta ma su. (Muslim ya ruwaito shi daga Abu Huraira Radiyallahu Anhu).

Mu sani cewa, ba wani bala’i da ya taba saukar ma jama’a face saboda zunubinsu ne. kuma Allah bai dauke bala’i sai da yin tuba. Allah Tabaraka Wa Ta’ala ya kira mu zuwa ga yin tuba yana mai cewa: “Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku mummunai ko da zaku samu rabauta” Suratun Nur: 31

Kuma ya ce:

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku tuba zuwa ga Allah tuba ingatacce” Suratut Tahrim: 8

Ya kuma yi alkawalin in mun roke shi gafara yana karba.

“Kuma duk wanda ya aikata laifi ko ya zalunci kansa sannan ya roki Allah gafara zai samu Allah mai yawan gafara ne, mai yawan jinkai” Suratun Nisa’i: 110

Zunubi yana da hatsari ba a lahira kawai ba ko a nan duniya. Daga cikin hadarin zunubi akwai: Haramta ma mutum jin dandanon ibada, da sa kuncin rayuwa, da tsukewar zuciya, da raunin jiki, da fadawa cikin matsala, da hana karbar addu’arsa – sai mutum ya yi ta rokon Allah bai ganin ijaba – da gushewar ni’imomin Allah, da mummunan karshe da azabar lahira. Haka kuma mai sabo in ya kai wani lokaci ya kan saba da shi ya daina ganin girman sa, ya yi fatali da shi; ya manta da girman wanda ya saba ma. Daga nan sai ayi ma sa istidraji, kwatsam! Sai mutuwa ta riske shi ayi ma sa mummunar damka.

Zunubi duka aikin shedan ne. kuma alkawali ya yi da kakkarfar rantsuwa da Allah mahalicci cewa, sai ya halaka ‘yan adam gaba daya ta hanyar sabo, sai fa wanda Allah ya yi ma sa gamon katar. To, a cikin rahamar Allah sai ya shar’anta muna yin tuba don mu kubuce daga igiyar shedan mu koma wurin mahaliccinmu. Kuma Allah Tabaraka Wa Ta’ala na murna da bawansa idan ya tuba fiye da murnar wanda kishirwa za ta halaka a jeji sai ya tsinci abin hawansa da ruwansa, ya yi tsalle yana murna har ya yi tuntuben harshe wajen gode ma Allah. Wannan na nuna ma na yadda Allah ke son bayinsa da kuma jin tausayinsu. Mu yi nazarin wannan aya da kyau, in da buwayayyen sarki Allah ke cewa a cikin kissar Ashabul Ukhdud wadanda suka yi wa muminai mummunan kisa ta hanyar azabta su da wuta, haka suddan ba wani dalili sai don suna kiran Allah. Ga abinda Allah ya ce a game da su:

“Hakika wadanda suka fitina mummunai maza da mata sannan ba su tuba ba, to suna da azabar jahannama, kuma suna da azabar gobara” Suratul Buruj: 10

Wadannan fa bayinsa suka kashe mutanen kirki ta hanyar azabtar da su cikin wuta amma ga Allah Ta’ala na nuna ma su hanyar tuba.

Shedan – a cikin nasa dabaru – ya kan ribaci wasu mutane idan ya ga ba makawa zasu tuba, sai ya kawata ma su wani zunubin wanda zai nuna ma su ya fi sauki, ko wanda sun fi iya shi ko sun fi samun ikon yin sa lamui lafiya, ko don shi aka fi yi a yankinsu, ko don shi ne irin aikin abokansa. Wanda ya tuba don Allah ba zai canza sabon da ya bari da wani ba sai dai ya bar shi gaba daya don neman yardar Allah da samun sakamakonsa.

Ya ku bayin Allah! Tuba yana da sharudda wadanda suka hada da jiya da yau da gobe:

a. Jiya: Yin da-na-sani a kan zunubin da ya yi da jin zafin yin sa.

b. Yau: Dakatar da yin sa nan take.

  1. Gobe: Kakkarfar niyya ta barin aikata shi har abada.

d. Idan kuma wani alhaki na dan adam ya rataya a wuyansa ya sauke shi ta hanyar mayar da kayan da aka yi zaluncin su ko bada damar mutum ya fidda hakkinsa ko a nemi afuwarsa. Ko wanda ya cuta ma iyalansa ta hanyar hana su alhakinsu, idan ya tuba dole ne ya ba su hakkinsu.

Haka kuma tuba na da wasu ka’idodi da ya wajaba mai tuba ya kula da su:

1. Yin tuba don Allah ba don wata manufa ba ko don kasawa ga sabo ko rashin abinda zai sa ayi sabon. Wanda ya bar sabo misali don tsaron mutuncinsa a idon jama’a to ba za a rubuta ma sa ladar tuba ba. Wanda ya bar Zina don gudun kamuwa da miyagun curutoci ba za a rubuta ma sa ya yi Zina ba amma kuma ba zai samu ladar tuba don Allah ba. Haka wanda ya ki karbar cin hanci don kar ya bata sunansa ko gudun ya fada hannun hukumomin kula da masu karya tattalin arziki. To balai wanda ya bar shan giya don likita ya hana shi ko don ba ya da abin sayen ta. Ko kuma mawakin da ke zagin mutane ko ya ke yin alfasha sai ya daina don an daina sauraren sa ko don ya yi tsufa ko ciwon da ba ya iyawa. Amma fa duka wadannan suna iya tuba a cikin wannan hali ta hanyar yin nadama a zuci kan abinda ya gabata da jin ciwon abinda suka riga suka aikata. Shi ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yake cewa: Tuba shi ne yin da-na-sani.

2. Gaggauta tuba da rashin yin jinkiri tunda mutum bai san lokacin da mutuwa za ta riske shi ba. Idan alkiyama karama ko babba ta tsaya ga mutum babu sauran tuba.

3. Dole ne wanda ya tuba ya ji munin abinda ya bari na sabo kar ya rinka tunowa da sabonsa na baya yana jin dadi watakila ma har da fatar ina ma zai sake?! Wanda ya yi wannan bai tuba ba.

4. Mai tuba yana da kyau kar ya amince da cewa kawai ya tuba, a’a, ya rinka tuna ya yi laifi kuma yana neman afuwar Allah, bai sani ba ko ya samu ko tukuna. Wannan zai sa mutum ya rinka ibada don neman kaffara tunda Allah ya ce: Lalle ayyukan lada na goge na zunubi.

5. Wanda ya tuba daga wani laifi na alhakin Allah dole ya tashi tsaye wajen ba da wannan alhaki. Kamar wanda bai bayar da zakkar dukiyarsa. Idan ya tuba dole ne ya fitar da hakkin Allah ya ba talakkawa.

6. Idan mutum ya tuba yana da kyau ya bi duk hanyoyin da za su hana shi koma ma sabo. Idan yana kusa da wurin sabon ne sai ya canza wuri, ko yana tare da masu sabon ne ya canza abokai, ko in yana da ababen sabon ne ya talafa su don kar su sa ya kwance tuba. Da yawa wanda ya tuba daga Zina misali amma ta hanyar hotunan da ya ajiye na abokan shashancin sa ko karanta wasu wasikunsu na soyayya ko sauraren wasu wakokin da suke saurare a tare can da sai ya tada tuba. Don haka dole ne ya dauki duk matakan da ke hana shi komawa baya daga cikin su har da canza abokai ya samu wasu na kirki da zasu taimaka ma sa kanIstikama.

7. Daga cikin abinda zai bayyana kyawon tuban mutum ya yi kokarin maye ayyukansa na barna da wasu ayyuka na alheri. Jikin da aka riga aka gina shi da Haram sai a yi kokarin sa shi yin da’ar Allah gwargwadon iko. Kudin da aka tara ta hanyoyi barkatai da ya-ki-halal-ya-ki-haram sai ayi ta kokarin sarrafa su ta hanyoyin da su ke yardar da ubangiji mahalicci.

Ya ku bayin Allah! Akwai da yawa wadanda ke son tuba amma shedan ya kan jefa ma su wasu tambayoyi domin ya kange su.

  • Wani zai ce, ko na tuba Allah bai karba. Don me? Ga shi ko Allah ya kira mu ga tuba kuma ya yi mana alkawalin karba!
  • Wani kuma sai shedan ya gwada ma sa girman zunubansa. Dan fashi ne ya kashe mutane masu yawa ya kwace dukiyoyi ba iyaka, barawo ne da bai iya kimanta abinda ya sata, mazinaci ne da ya bata ‘yan mata ba su lissafuwa, ya ci amanar mutane iri-iri da sauran ire-iren su. Wannan bai hana yin tuba ga wanda ya san girman rahamar Allah da yadda yake son mai tuba.
  • Wani kuma shedan ya kan ce ma sa: Ya zaka yi da abokanka? Amsar da ya kamata a ba shedan a nan ita ce, Allah na fi so ko abokaina?
  • Wanda ya fi wannan hadari da wahala shi ne wanda ya aikata wasu miyagun ayyuka da aka yi rikodin din su. A kullum shedan zai rinka ma sa barazana da cewa, idan ka tuba abokanka suka tona asirinka fa? Sanin wannan ya sa Yahudawa a kullum suke kokarin su aukar da shugabanninmu cikin ma’asi idan sun je garuruwansu, kuma suna kokarin ta ko wace hanya suyi rikodin din su don in ta kama a gaba. Kar a amince da su. Suna da hanyoyi na zamani masu wuyar kubucewa. Allah ya kare mu. Wanda ya fada a wannan tarko kuma kar ya fasa tuba, makiyansa rundunar shedan ne kawai, nan take Allah zai watse mai su. Ka tuna cewa, Allah yana son masu tuba kuma yana tare da su. Wannan shi ne abinda ya faru ga Marthid al Ganawi, sahabin da ya rinka dauko raunanan musulmi daga Makka yana taimaka ma su yin hijira sai rannan tsohuwar karuwarsa ta jahiliyyah ta kama shi ta yi masa kuwwa har aka yo ciri a kan sa, amma nan take Allah ya rufe idanunsu daga gare shi har ya samu ya kubutar da bawan Allan da ya zo wa ceto. Idan har ya zama dole, fito fili mana, ka ce: na yi amma yanzu na tuba na koma ma Allah, sai me? Kunyar duniya ce ta fi hadari ko ta lahira?
  • Wani kuma shedan zai ce ma sa, to kai laifinka ai haddi ne Allah ya sa ma shi. Idan ka tuba dole ne a jefe ka, ko a katse ma ka hannu tun da kayi sata, ko ayi ma ka bulala tun da ka yi kazafi! Wani mutum ya yi niyyar tuba daga sata sai ya tambayi limamin masallacinsu sai ya ce ma sa to, dole ne sai an yanke ma ka hannu! Don haka dole sai ya fasa. Subhanallahi! Ba kowane mai ba da sallah ko kiran sallah ko ma mai wa’azi ya kamata a tambaya ya yi fatawa ba. Irin wadannan bata garin malamai barnarsu ta fi gyaransu yawa.
  • Wani kuma ya tuba, amma kullum sai shedan ya rinka bata ma sa rayuwa, yana tuna ma sa abinda ya yi can baya don ya sa shi cikin damuwa. Idan ka ji haka, to, ka sani tubanka ya yi kyau kenan, domin da-na-sani shi ne tuba.
  • Wani kuma yana son ya tuba daga wani zunubi amma bai iya barin wani zunubin na daban sai shedan ya nuna ma sa gara ma ya hakura har sai sadda zai iya barin duka sabo.
  • Wannan shi kuma ya taba yin tuba amma sai shedan ya rinjaye shi har ya sake komawa. Daga nan kuma sai ya gwada ma sa cewa, ai kai tuba gare ka bai yuwa don kamar kana izgili ne da ubangiji tunda ko yaushe tuba za ka rinka yi kana tayarwa.

Duka wadannan hanyoyi ne da shaidan yake bi ya ci galaba a kan mu ya hana mu tuba. Wajibi ne mu tuba tun gabanin a shamakance mu daga tuba a lokacin da Allah yake cewa: “Kuma aka sa shamaki tsakanin su da abinda suke shawa kamar yadda aka yi ma ire-irensu can da. Hakika sun kasance cikin shakka mai rikitarwa” Suratu Saba’i: 51-54

Ya ku bayin Allah! Akwai abubuwan da ke kara ma zunubi kaimi ya kara zama hadari ga mai yin sa:

  • Daukar zunubi da sassauci da rashin jin nauyin sa.
  • Dagewa a kan sa. Shi ya sa malamai suka ce: laifi ba ya girma in ana tuba, ba ya karanci in aka nace a kan sa. (Hadisi ne da Dailami ya ruwaito shi daga Ibnu Abbas amma bai inganta ba. Duba: Silsilatul Ahadis Ad Da’ifa na Albani, Hadisi na 4810 (10/351).
  • Yin takama da tinkaho da nuna jin dadi da yarda da yin sabo.
  • Haka kuma sabo na kara muni idan aka bayyana abinda Allah ya suturta. Kamar mutumin da zai yi sabon sa a asirce, kuma Allah ya rufa shi sai ya zo yana tona kan sa.
  • Haka duk wanda ke tallata barnarsa yana kawata ta ga jama’a don ya sa ma su sha’awar ta.

Zunubi kamar ciwo ne; mataki mataki ne. Akwai wanda ke bukatar ‘yan kwayoyi kadan sai ya ba da baya. Akwai mai bukatar kulawar likitoci da shawarwari da nacewa ga shan magani. Wani ciwon sai an yi tiyata an fede an cire shi. Kowane dan adam yana da wani nau’i na laifi ko kasawa da yake fama da shi. Sai dai wani in ya yi laifi nan take ya karaya, ya fara tsarguwa da jin tsanar kan sa a kan sanin ya yi laifi. Wani kuma har murna yake yi ya samu sa’ar biyan bukatarsa. Wani na tunanin bari, wani ba shi yi. Wani na rufa-rufa da zunubinsa yana boyewa, wani ko har fira ya ke yana bayyana kansa. Daga nan zamu gane nisan wasu daga tuba ya fi na wasu. Kada mu yi tsammani ya ku bayin Allah cewa, ‘yan caca ne kawai za su tuba, ko barayi ne za su tuba, ko fitattun masu laifi a cikin al’umma. Mutanen kirki ma na bukatar tuba, waliyyai da Annabawa da kowa ma na bukatar tuba. Kamar yadda Allah ya ce: “Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya ya ku mummanai ko da zaku samu rabauta” Wanda duk bai tuba ba to, ya sani yana cikin azzalumai:“Kuma duk wanda bai tuba ba to, wadannan su ne azzalumai”.

Ya ku bayin Allah! Akwai wani zunubi mai hadari da ya tuzgo a cikin hadisi cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya ce: Allah ya hana masu yin sa tuba. Wani irin zunubi ne wannan? Ya kai matuka ga zama hadari, kuma ya wajaba mu san shi. Wannan zunubi shi ne Bidi’a! (Duba: As Sunnah na Ibnu Abi Asim, shafi na 37 da Silsilatul Ahadis As Sahiha hadisi na 1620). Dan bidi’a shi ne wanda yake barin umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam da gangan don ra’ayin wani ko ra’ayin kashin kansa. Allah Ta’ala kuwa cewa ya yi:

“Wadanda suke saba ma al’amarinsa to, su ji tsoron fitina ta same su ko azaba mai radadi” Suratun Nur: 63

Wannan shi ne ma’anar cewar da Allah Ta’ala ya yi a Suratul Anfal:24

“Ya ku wadanda suka yi imani! Ku karba kiran Allah da manzonsa idan suka kira ku zuwa ga abinda ke raya ku. Kuma ku sani hakika Allah yana sanya shamaki tsakanin mutum da zuciyarsa, kuma hakika zuwa gare shi ake tayar da ku” Suratul Anfal: 24

  Ya ku bayin Allah! Ku sani, Allah ya sawwake mana tuba sabanin yadda ya yi ga al’ummomin da suka gabace mu wadanda tuban dayansu shi ne ya kashe kansa. Iyakacin tubanmu – al’ummar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam – mu yi da-na-sani, mu surmuya kasa muna masu ba Allah hakuri. Kuma mu sani cewa, duk wanda ya tubar ma Allah daga wani zunubi, to, Manzon AllahSallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam ya sunnanta ma sa yin alwala da nafila raka’a biyu a cikin natsuwa domin cikon tsarkin sa da neman gafarar ubangijinsa. Yana da kyau kuma bayan haka mutum ya yi istigfari da sadaka da gabatar da wasu ayyukan alheri domin su yi ma tubansa rakiya. (Duba Salatut Taubah na Sheikh Abdallah bin Jibrin, shafi na 10).

Ya Allah! Ka sanya tuba ya zamo karshen ayyukanmu. Ya Allah! Ka sanya alheri ya zamo shi ne cikamakin aikinmu. Ya Allah! Ka sanya ranar haduwa da kai ta zamo ita ce  ranar farin cikinmu.

An gabatar da ita a ranar Jum’ah 13TH Rajab 1431H

MU KOMA MA ALKUR’ANI

Leave a comment

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Ya al’ummar musulmi! Alkur’ani littafin Allah ne na karshe wanda ya ke da dimin dimin saukowar sa daga wurin Allah. Amintaccen littafi ne, tsararre, tsarkakakke, wanda ba mai iya kara kome ko ya canza wani abu – koda wasali ne – a cikin sa. Haka kuma littafi ne mai albarka, mai saukin karatu da saukin fahimta, wanda Allah ya yassare ma masu bukata. Gaskiya ce zallar ta, adalci ne tsagwaron sa, shiriya ce gangariya wadda kowa ya saba mata to ya shiga tekun demuwa da gigita.

Allah da kan sa ne ya tsare Alkur’ani, sai ya samar da mazaje a kowane zamani da mata masu hardace shi. Tun da dadewa an bi diddigin surori da kalmomi da ma haruffan Alkur’ani, an tantance su ta yadda babu mai iya wani shisshigi ko kaudi na kari ko ragi a cikin sa. Masana Alkur’ani sun kasa shi juzu’i 30, hizifi 60, Nisifi 120, Rubu’i 240, Thumuni 480. Sannan sun bayyana adadin surorin sa 114 ne, ta farko ita ce Fatiha, ta Karshe Suratun Nasi. Idan ka zo Suratul Hadid, sura ta 57, to ka zo karshen rabin Alkur’ani. Suratul Mujadala ta 58 ita ce farkon rabi na biyu. Ayoyin Alkur’ani 6,616 ne. Bismillah ita ce ta farko,(من الجنة والناس) ita ce ta karshe. Ayar da ta ke tsakiyar Alkur’ani ita ce aya ta 45 a cikin Suratus Shu’ara’i (فألقى موسى عصاه فإذا هي تلقف ما يأفكون) Aya ta 46 kuwa (فألقي السحرة ساجدين) tana a kashi na biyu na Alkur’ani. Kalmomin Alkur’ani ma an kididdige su, an samu kalma 77,934. Kalma ta farko ita ce ب wadda ke cikin بسم الله ta karshe ita ce الناس ta karshen Suratun Nas. Idan ka zo daidai kalmar (ﯫ) a aya ta 19 Suratul Kahf to ka zo tsakiyar kalmomin Alkur’ani. Haruffan Alkur’ani su kuma 323,671 ne. Idan ka zo kan harafin ن da ke cikin (نكرا) a aya ta 74, Suratul Kahf to, ka zo tsakiyar haruffan Alkur’ani. Wannan Nun ita ce harafi na 38,967, Kaf tana a kashi na biyu na Alkur’ani.

Ya al’ummar Musulmi! Littafin nan da yake da sura 114 kowace tana farawa da Bismillah in ban da sura guda daya ita ce Suratut Taubah. In da wannan Alkur’ani abin wasa ne da yanzu an samu wanda ya yi kaudin rubuta Bismillah a wannan sura. Allah ya yi gaskiya da yake cewa:

((ما ننزل الملائكة إلا بالحق وما كانوا إذن منظرين * إنا نحن نزلنا الذكر وإنا له لحافظون)) سورة حجر: 8-9

Karatun Alkur’ani ciniki ne babba mai cikakkar riba. Allah Ta’ala ya ce:

“Lalle ne wadanda ke karanta littafin Allah kuma suka tsayar da sallah kuma suka ciyar daga abinda muka azurta su a asirce da bayyane suna fatar yin kasuwanci da ba zai taba yin tasgaro ba. Domin Allah ya cika masu ladarsu kuma ya kara masu daga cikin falalarsa. Hakika shi mai yawan gafara ne, mai yawan godiya” Suratu Fatir: 29-30

Manzon Allah Sallallahu Wasallam ya bayyana mana irin tanadin da Allah ya yi mana a kan karanta wannan littafi mai albarka. Tirmidhi ya fitar da hadisi kuma ya inganta shi ta hanyar Abdullahi bin Mas’ud Radiyallahu Anhu wanda ya ce, ya ji Manzon Allah Sallallahu Wasallam yana cewa: Duk wanda ya karanta harafi daya na littafin Allah to, yana da lada wacce za a ribanya ta sau goma. Ya ce, kuma ba ina nufin wanda ya ce Alif Lam Mim, ya yi kalma daya ba, a’a ko wanensu kalma ne. Duba Sunan At Tirmidhi 2/505 da kuma Sahihul Jami’ na Albani 3/203. Bisa ga wannan duk wanda ya samu saukar Alkur’ani guda daya, ya ratsa kalmominsa 77,934 da kuma haruffansa 323,671 to, ya saka credit a account dinsa na lada 3,236,710.00. Wanda kuwa ya hardace Alkur’ani a kan sa to, za a kira shi ranar Alkiyama a bainar jama’a, a sanya masa kanbe iri-iri, a ba shi lambar girma, a tabbatar masa da yardar Allah, sannan a umurce shi da ya shiga aljanna, ya fara tilawar sa a daidai lokacin da yake dagawa zuwa matakan girma da daraja a aljanna, ba zai tsaya ba sai inda tilawarsa ta kare, nan ne masaukinsa na aljanna. Duba: Sunan At Tirmidhi, hadisi na 3914 da Abu Dawud 1464 da kuma Silsilatul Ahadis As Sahiha, hadisi na 2240. Akwai kuma surorin Alkur’ani da suke kawo dauki su ceci wanda ya hardace su a alkiyama koda bai hardace Alkur’ani dukan sa ba.

Ya al’ummar musulmi! Mu sani, Allah Ta’ala ya yi mana duk gatanci da ya saukar mana da wannan Alkur’ani. Ya sawwake mana shi domin karantawa da fahimta. Amma kuma Allah ta’ala ya bada labarin cewa, Manzonsa Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam zai yi koke game da wasu daga cikin al’ummarsa da suka kaurace ma Alkur’ani. Kaurace ma Alkur’ani na nufin rashin gode ma wannan karimci na madaukakin Sarki. Duk wanda ba ya samun lokacin da zai ware ma Alkur’ani domin ya karanta shi to, ya kaurace ma Alkur’ani. Haka ma duk wanda yake karanta Alkur’ani ba bisa ga ka’idodinsa na tajwidi ba shi ma ya kaurace ma Alkur’ani. Wanda ke karanta shi cikin hanzari da rashin natsuwa shi ma ya kaurace ma Alkur’ani. Haka duk wanda bai tadabbur nazarin ma’anonin Alkur’ani shi ma ya kaurace ma Alkur’ani. Wanda ko yake karanta shi amma ya yi biris da iyakokinsa shi ma ya kaurace ma Alkur’ani.

Alkur’ani cikakken tsari ne na rayuwa wanda ya bayyana ma dan adam yadda ya kamata ya yi hulda da mahaliccinsa da kuma yadda ya kamata ya yi hulda da mutane ‘yan uwansa. Kai ba ma mutane ba har dabbobi da kwari da tsuntsaye, Alkur’ani ya shata yadda dangantakar mu ya kamata ta kasance da su. Alkur’ani ya fada ma mutum yadda ya kamata ya kula da jikinsa ta fuskar tsafta da kiyon lafiya. Ya fadi irin dangin abinci da abin sha da ya kamata mutum ya ci ko ya sha da wanda bai kamata ba. A cikin sa akwai tsarin Ibada da na Mu’amala ta cinikayya da auratayya da dokoki na tsawatarwa da haddi ga masu aikata ayyukan assha masu bata rayuwar al’umma. Tsarin tattalin arzikin da Alkur’ani ya shimfida shi kadai ne wanda ba a samun zalunci cikin sa. Tsarin zamantakewar da ya shata shi kadai ke iya samar da tsaro da zaman lafiya tsakanin jama’a. Tsarin siyasar sa shi kadai ne ke iya tabbatar da adalci. A kowane abu na rayuwa Alkur’ani ya gwadi hanya mafi shiriya da mikewa a cikin sa. Duba abinda Allah ya ce a Suratul Isra’i: 9 da kuma Suratu Ibrahi: 1

Ya ku jama’ar musulmi! Duk wanda zai karanta Alkur’ani dole ne ya lura da ladubban karatun sa, ya kiyaye su don samun irin tanade-tanaden da Allah ya yi, kuma don samun shiriya a cikin sa. Ga kadan daga cikin wadannan ladubba:

1. Tsarkake zuciya, da yi don Allah, tare da kauce ma duk wata manufa wadda ba neman yardar Allah ba da samun lada a wurin sa.

2. Wanke zuciya daga cututtukan da ka iya samun ta wadanda ke sa ta dushe, ta kasa karbar hasken Alkur’ani, kamar ciwon kyashi da annamimanci da keta da rashin tausayi da makamantan su. Haka ma duk wani zunubi wanda mutum zai yi shi da daya daga cikin gabban da ke karbar tilawar Alkur’ani, wato gabaiban ji da gani da furuci da fahimta, ina nufin zuciya da kunnuwa da idanu da harshe, to wannan yana rage basirar fahimtar Alkur’ani da tasirantuwa da shi.

3. Mayar da hankali a lokacin karatu, da barin wasa da hannu ko kafa ko shagaltuwa da kallo ko sauraren wani abu ko jiran kira daga handset ko makamancin su sai in da lalura mai karfi.

4. Karanta Alkur’ani a cikin tsarki da cikakkiyar alwala, a wuri mai tsafta, da zaman ladabi da fuskantar alkibla, ya kuma karanta shi ba da gaggawa ba.

5. Tunani mai zurfi game da ma’anonin Alkur’ani musamman ga wanda ke iya gane ma’anarsa kai tsaye kowa gwargwadon ikon sa. A nan halartar wuraren tafsirin Alkur’ani na da matukar amfani.

6. Kula da alakar kowace aya da hawa da gangarar karatu, ta hanyar duba siyakin da aya ta zo a cikin sa da ayoyin da ke gaban ta da bayan ta. Haka ma duba alakar karshen aya da farkonta, musamman masu karewa da sunayen Allah.

7. Mai karatu ya aiwatar da ka’idodin tajwidi gwargwadon saninsa da iyawarsa ba tare da ya bari sun dauke hankalinsa daga tunanin ma’anoni ba.

8. Mai karatu ya ji cewa, Alkur’ani yana magana da shi ne kai tsaye, ko umurni ya ke bayarwa ko labari.

9. Kokarin tasirantuwa da kowace aya idan ya karanta ta. Idan an kira aljanna ya ji shaukin ta, idan wuta ce ya ji razani, in an bada labarin kafirai da yadda suke karyata Annabawa sai haushin su ya kama shi, in an fadi wani halin kirki ya nasa a rayuwarsa zai sifaitu da shi, idan an hana wani aiki na laifi sai ya auna kan sa, ya kuma yi niyyar ba zai sake yin sa ba in har ya taba yi can a baya.

10. Mai karatu ya cire jin kai da tunanin girma a lokacin tilawa, ya ajiye kansa a matsayinsa na bawan Allah mai neman jinkayinsa da rahamarsa, mai kuma jiran a ba shi umurni don ya aikata.

Duba wasu daga cikin ladubban nan a Fara’idul Jalila na Sheikh Abdullahi dan Fodio.

Ya ku bayin Allah! Da irin wadannan ladubban ne magabata suka kasance suna karanta Alkur’ani kuma suna sauraren sa, suna tasirantuwa da shi kuma suna tasiri a kan duk wanda ya saurara. Duba asalin musuluntar sayyidina Umar a kan ya ji ana karatun ayoyin farkon Suratu Daha. Duba kuma dalilin musuluntar Jubair bin Mud’im wanda ya zo don ya nemi fansar mushrikai da aka kama fursunoni a yakin Badar sai ya iske Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam yana karanta Suratur Dur, ya kuwa kasa kunne yana saurare Alkur’ani yana kama jikinsa, har sai da ya iso aya ta 7 zuwa 8 sai ya ji kamar zuciyarsa za ta tsage saboda tsoro, nan take kuma ya musulunta. Mu karanta tarihi za mu ga bayin Allah da dama wadanda Allah ya karbi rayuwarsu suna karanta Alkur’ani a cikin sallah ko a wajenta. Saboda sun mayar da tilawa babban bukinsu, sai Allah ya yi masu tukuici da sanya ta ta zamo karshen rayuwarsu, domin a tashe su a cikin ta. Duba misali littafin Al Kamil na Ibnu Adi (19/67).

 

Ya ku musulmi! Karanta Alkur’ani da tunani game da ma’anoninsa da asirransa suna amfani ne idan an yi aiki da dokokin da Allah ya shata na ibada da zamantakewa da sauran huldodin rayuwa  a cikin sa. Ina amfanin wanda zai karanta Alkur’ani amma ya yi biris da dokokinsa? An ce ayi, ya kiya, an ce a bari ya ki bari! Ina girma ga al’ummar da Allah ya ba ta wannan littafi mai albarka amma tana zuwa wasu kasashe don neman agaji ga tsara dokokin ta? Ko tana shata ma kan ta wasu dokoki daga son rayuwar wasu daidaiku a cikin ta?!

Allah Ta’ala ya ce: Kuma mun saukar maka da littafin yana mai bayanin ga kome da kome da shiriya da rahama da bushara ga musulmi. Suratun Nahl: 89

Ya ku al’ummar musulmi! Girmama malaman Alkur’ani da makarantansa wajibi ne. kula da ci gaban karatunsa da kyautata shi aiki ne mai kyau da ake bukatar mu hada kai a cikin sa. Shirya gasar karatun Alkur’ani bisa ga wannan manufa don karfafa guiwar masu karatu da jawo hankalin masu rafkana da lurar da jama’a muhimmancin sanin ka’idojin tilawa abu ne kyakkyawa da yake tabbatar da manufar shari’ar musulunci. Kuma karfafa wannan na daga cikin taimakon addini da ake samun lada a kan sa. Amma fa dole ne muyi nuni zuwa ga wajabcin tsarkake niyya ga masu karatu da masu bada kyauta. Duk wanda ya yi don Allah aikinsa mai kyau ne, wanda ko ya yi da wata manufa kamar samun kudi ko daukakar suna, ko yin alfahari, to ya saba ma Allah don ya shigar da wanin Allah a cikin aikin ibada. Alkalai su sani cewa, yadda duk ake hukunta alkalan kotuna haka Allah zai hukunta su ranar alkiyama, zasu kubuta idan sun yi adalci, zasu kuma sha wuya idan sun kauce ma sa. Masu shirya gasa da masu kula da gudanar da ita (Co-odinators) kowa ya yi kokari ya sauke nauyin da aka aza masa.

Mu koma ma Alkur’ani ya ku jama’ar musulmi, zamu samu warakar duk curutocinmu a cikin sa. Mu koma ma Alkur’ani, zamu samu nagartaccen tsarin rayuwa a cikin sa. Mu koma ma Alkur’ani, zamu samu warwarewar duk matsalolinmu a cikin sa. Mu koma ma Alkur’ani, zamu samu kwanciyar hankali, da daukaka, da ci gaba da wadatar arziki da yardar Allah.

Allah ya yi muna dace, ya sa Alkur’ani ya zamo jagoran mu zuwa aljanna.

An gabatar da ita a ranar juma’a 30TH Jimada Ula 1431H

Older Entries